1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin sabon Firaministan kasar Australiya

September 24, 2013

An haifi Tony abbott sabon Firaministan kasar Australiya ranar hudu ga watan Nowamban shekarar 1957, wato yanzu yana da shekaru 55 da haihuwa.

https://p.dw.com/p/19mob
Hoto: Reuters

An haife shi a birnin London na kasar Birtaniya. Ranar bakwai ga watan Satumban shekarar 1960 yana da kusan shekaru uku da haihuwawa iyayensa sun koma Australiya, inda mahaifiyarsa ta fito, yayin da mahaifinsa yakasance dan Newcastle.

Abbott ya halarci makarantun Firamari da Secondary, kafin daga bisani ya zarce zuwa jami'ar birnin Sydney inda ya samu digiri kan fannin tattalin arziki, sannan ya sake samun wani digirin kan bangaren shari'a.

Kafin ya tsunduma cikin harkokin siyasa Tony Abbott ya yi aikin jarida na wani lokaci. Ya shiga cikin harkokin siyasa gadan-gadan a farkon shekarun 1990. Ya lashe zabe majalisa karkashin jam'iyyar Liberal a shekarar 1994, yayin zaben cike gurbi.

Tsakanin shekarar 1996 zuwa 1998 Abbott ya rike mukamai daban-daban da suka hada da ministan Kwadago, da Ministan Ilimi, da Ministan kula da rayuwar Matasa. Ya kuma sake rike mukaman ministan a kasar ta Australiya daga shekara ta 2003 zuwa 2007, da suka hada da Ministan kula da Muhalli da Ministan Lafiya da kula da tsaffi, duk karkashin Firamnistan John Howard.

A matsayinsa na shugaban Liberal ya zama shugaban 'yan adawa ranar daya ga watan Disamban shekara ta 2009. Ya ci gaba da zama a matsayin yana adawa da Firaministan Kevin Rudd da kuma Julia Gillard na jam'iyyar Labour, wadanda suka jagoranci gwamnatin kasar ta Australiya lokuta daban-daban bisa sauyin shugabanin jam'iyarsu da aka samu.

Likafar Tony Abbott ta ja gaba yayin zaben ranar bakwai ga wannan wata na Satumba, inda jam'iyyar Liberal da wadanda suka kawance suka samu nasarar kawar da Kevin Rudd daga madafun iko. An rantsar da abbott kan mukamin firaminista ranar 18 ga wannan wata na Satumba tare da majalisar ministocinsa. Kuma ya zama firamnista na 28 da aka yi a kasar ta Australiya.

A bangaren iyali, Tony Abbott yana da mata da 'ya'ya uku.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu