1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu

Ahmed Salisu MNA
March 25, 2019

Shirin Amsoshin Takardunku ya amsa tambaya kan tarihin shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta Farfesa Mahmood Yakubu.

https://p.dw.com/p/3Fbrv
Nigeria - Verschiebung der Präsidentschaftswahlen
Hoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

An haifi Farfesa Mahmood Yakubu a shekarar 1962 a jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Tarayyar Najeriya kuma ya yi karatunsa ne na firamare a makarantar firamare ta Kobi da ke cikin garin na Bauchi daga bisani kuma sai ya tafi kwalejin horas da malamai da ke garin Toro a jihar ta Bauchi dai inda nan ne ya kamala karatunsa na sakandare. Ta fuskar karatun jami’a kuwa, Farfesa Yakubu ya yi karatunsa na digirin farko a jami’ar Shehu Usmanu Danfodio da ke jihar Sokoto a arewa maso gabashin Najeriya din inda ya karanta ilimin tarihi.

Farfesa Mahmood Yakubu ya kuma yi karatunsa na digiri na biyu a Kwalejin Wolfson da ke Cambridge a Birtaniya inda ya karanci ilimin hulda kasa da kasa inda ya kamala a shekarar 1987. Ya kuma yi digirnsa na uku a a fannin tarihin Najeriya a Jami’a Oxford da ke Birtaniya inda ya kammala a shekarar 1991.

Nigeria Prof. Mahmoud Yakubu (L) Präsident Muhhamadu Buhari
Hoto: Imago/Zuma

Ta fuskar aiki kuwa, Farfesa Mahmood Yakubu ya shafe tsawon lokaci yana koyarwa a kwalejin horas da sojojin Najeriya da ke Kaduna inda yake ware wajen koyar da dabaru na dakile yakin sari-ka-noke da kuma abubuwan da suka danganci tarihi da huldar kasa da kasa.

Farfesa Yakubu ya rike mukamin mukaddashin sakataren kudi da mulki na taron kasa da aka yi a tarayyar Najeriya a shekarar 2014, kuma daga bisani wato a watan Oktoban shekarar 2015 ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC.