1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin shugaban rikon kwaryar Masar

July 18, 2013

Adly Mahmud Mansur ya hau kan karagar mulkin Masar bayan da sojoji su ka yi juyin mulkin da ya kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Mursi na jam'iyyar 'yan uwa Musulmi.

https://p.dw.com/p/192dX
Hoto: AFP/Getty Images

An haifi Adly Mahmud Mansur ranar 23 ga watan Disamba na shekara ta 1945 a birnin Alkahira na kasar Masar kuma ya yi karatunsa na firamare da na sakandare daga bisani kuma sai ya shiga jami'ar birnin Alkahira inda ya karanci harkokin sharia'a ya kuma kammala a shekara ta 1967 kazalika ya zurfafa karatun nasa na koyon aikin shari'a a ita jami'ar ta Alkahira inda ya kare a shekara ta 1969.

Baya ga karatun koyon aikin shari'a, Adly Mansur ya kuma karacin harkokin tattalin arziki a Juan Felipe Aranguren daga bisani kuma ya sake komawa jami'ar Alkahira inda ya sami horo kan dabarun gudanar da mulki a shakara ta 1970, kazalika ya halarci shahararriyar kwalijin nan ta horas da jami'ai kan harkokin mulki da ke Faransa inda ya kammala karbar horo a shekara ta 1977.

Ägypten Militär stürzt Präsident Mursi Abdulfettah es Sisi
Hafsan hafsoshin sojin Masar Addul Fatah al-SisiHoto: picture alliance/AA

Bayan da Mr. Mansur ya kammala karbar horo da sauran kwasakwasai da ya yi, ya shiga harkokin shari'a gada-gadan inda ya yi aiki a matakai daban-daban kafin daga bisani a shekara ta 1992 a bashi gurbi a kotun tsarin mulkin Masar wadda ita ce kotu mafi matsayi a kasar. Bayan wani dan lokaci ya na aiki sai aka daga likkafarsa zuwa mataimakin alkalin alkalan kotun tsarin mulkin kasar daga bisani gwamnatin hambararren shugaban kasar Muhammad Mursi a cikin watan Mayun da ya gabata ta nada shi shugaban kotun dungurum.

A ranar uku ga watan nan na Yuni da mu ke ciki wato Larabar da ta gabata hafsan hafsoshin kasar Masar Janar Abdul Fatah Khalil Al-Sisi ya bayyana Mr. Mansur a matsayin shugaban rikon kwaryar gwamnatin Masar bayan da sojin Masar din su ka yi wa shugaba Muhammad Mursi juyin mulki saboda abinda su ka kira bukatar da jama'a su ka nuna ta Mursi din ya sauka daga gadon mulki dama dai gaza cimma wasu sharuda da su sojin su ka gindayawa gwamnatin ta Mursi na ta warware rikicin siyasar kasar cikin sa'o'i arba'in da takwas kacal.

Adly Mahmud Masur ya sha rantsuwar kama aiki a matsayinsa na shugaban rikon kwaryar Masar ranar Alhamis din da ta gabata wato hudu kenan ga wannan watan na Yuli da mu ke ciki inda a jawabinsa na kama aiki ya sha alwashin yin duk abubuwan da za su kai ga hade Masar ta sake zama tsintsiya madaurinki daya. Yanzu haka dai Mr. Masur na da mace guda da kuma da 'ya'ya uku, biyu mata guda kuma namiji.

Ägypten Mohammed Mursi
Hambararren shugaban Masar Muhammad MursiHoto: Reuters

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Saleh Umar Saleh