1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin tsohon shugaban Honduras

December 15, 2009

Tarihin tsohon shugaban Honduras: cikakken sunan tsohon shugaban na Honduras dai shine Jose Manuel Zelaya Rosales, kuma an haife shi a ranar 20 ga watan Satumban shekarar 1952

https://p.dw.com/p/L2Lo
Tsohon shugaban ƙasar Honduras Manuel ZelayaHoto: AP

To cikakken sunan tsohon shugaban na Hoduras dai shine Jose Manuel Zelaya Rosales, kuma an haife shi a ranar 20 ga watan Satumban shekarar 1952 a wani gari mai suna Juticalpa a yankin Olancho. Zelaya ya kasance babba daga cikin 'ya'ya huɗu da mahaifin sa ya haifa.Bayan daya isa shiga makaranta, an saka shi a makarantar Firamare mai suna Nino Jesus de Praga lius Landa. Kuma bayan kammala sakandare ya halarci Jami'ar ƙasar ta Hoduras inda ya fara karatun injiniyan gina hanyoyi.

Kuma kamar yadda tarihi ya nuna Manuel Zelaya dai ɗan wani hamshaƙin ɗan kasuwa ne dayayi suna wajen cinikin katako da kiwon dabbobi da harkokin noma. Wannan nema yasa Jose Manuel Zelaya bai kammala karatun sa na jami'a ba, domin shiga harkokin kasuwancin mahaifinsa.

Ƙasar Honduras da shi kansa Zelaya sunyi suna ne a idon siyasar duniya a ranar 28 ga watan Junin bana. Wannan ko ya faru ne bayan wani juyin mulki da sojojin ƙasar sukayi, wanda ya hamɓarar da shugaba Zelaya akan karagar mulki sakamakon wani yunƙuri da shugaban yayi na yin gyara ga kundin tsarin mulki ƙasar domin ƙara wa'adin mulkin sa, matakin da kotun ƙolin ƙasar tace haramtacce ne.

To sai dai Zelaya ya nuna taurin kai ga hukuncin kotun kuma ya ƙudiri aniyar gudanar da zaɓen raba gardama saɓanin hukuncin Kotun ƙolin. Amma ana jajibirin zaɓen ne kotun ƙolin ta bada umarnin a kama shi, kuma kafin kace kwabo sojojin ƙasar sun cafke shi, inda sukayi masa ɗaurin talala, amma kuma daga bisa ni suka tura shi gudun hijirah a ƙasar Costa Rica.

Wannan mataki da Sojojin ƙasar dake samun goyon bayan Majalisar Dokoki dama wasu 'yan jam'iyar tsohon shugaban bai samu goyon bayan sauran ƙasashen duniya ba, musanman ƙasashen yankin Amurka da suka haɗa da Amurka da Venezuela da Brazil da Costa Rica da dai sauran su, abinda ma yasa suka ƙaƙabawa ƙasar takunkumi.

Wannan ƙwarin guiwan da tsohon shugaban ya samu shine ma yasa ya ƙaddamar da wani mataki na komawa kan karagar mulkin ƙasar. A ranar 21 ga watan Satumba ne, al'uman Honduras suka wayi gari tare da ganin tsohon shugaban a ofishin Jakadancin Brazil, ɗaya daga cikin ƙasashen dake goyon bayan sa.

Wannan yasa aka shirya wani taron sasantawa tsakanin tsohon shugaba Zelaya da kuma shugaban wucin gadi Roberto Micheletti. Wanda ake fatan zai kai ga mayar da Zelaya akan karagar mulki kafin zaɓen 27 ga watan Nuwanban bana. Sai dai kuma daga bisani Majalisar Dokokin ƙasar tayi watsi da wannan yarjejeniya kuma aka gudanar da zaɓe a ranar 27 na Nuwanban, inda aka zaɓi sabon shugaban ƙasa.

Zaɓen da kuma ƙasashen Amirka da Costa Rica da sauran ƙasashen duniya sukace zasu mutun ta, saɓanin matakin da ada suka ɗauka na ƙin amincewa da zaɓen. Yanzu dai halin da ake ciki tsohon shugaban ƙasa Zelaya ya nemi yin gudun hijirah zuwa ƙasar Mexico, amma kuma dakarun gwamnati da sukayi wa ofishin jakadancin Brazil ƙawanye sun hana shi fita,lamarin da kuma ya sake buɗe wani sabon shafin rikicin siyasar ƙasar ta Honduras.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Yahouza Sadissou Madobi