1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taro a kan harkokin tsaro a Abuja

September 3, 2014

Ministocin harkokin waje na ƙasashen Benin da Kamaru da Chadi da Nijar da kuma Najeriya na gudanar da wani taro a kan samar da tsaro a yankin yammacin Afirka.

https://p.dw.com/p/1D5uj
Westafrikas Staatschefs bei ECOWAS Summit
Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

Taron ana gudanar da shi ne musammun ma dangane da ayyukan ta'addanci da Najeriya ke fuskanta na 'yan Ƙungiyar Boko Haram da ke barazanar ƙwace yankin arewa maso gabashin Najeriyar.

taron wanda ke zaman na bita bayan taron Paris da aka gudanar a cikin watan Mayun da ya gabata, zai tattauna game da inda aka kwana a kan kawo ma ƙasashen na Afirka ɗauki da ƙasashen duniyar suka yi alƙawari domin yaƙi da ta'addanci.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu