1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gipfel Damaskus

Leidholdt, Ulrich Amman (WDR) NEUSeptember 4, 2008

Assad ya yi fatan tattauna batun wanzar da zaman lafiya kai tsaye da Isra´ila

https://p.dw.com/p/FBZr
Shugaban Syria Assad da shugaba Sarkozy na Faransa a DamaskusHoto: AP

A yau a birnin Damascus shugaban Syria Bashar al-Assad ya buɗe wani taron ƙolin shugabannin ƙasashe haɗu da suka haɗa da shugaban Faransa Nikolas Sarkozy da Sarkin Qatar Sheikh Hamad al-Kalifa da Firaministan Turkiya Tayyip Erdowan. An shirya taron ne don yin musayar ra´ayoyi dangane da halin da ake ciki a yankin Gabas Ta Tsakiya. Assad ya ƙarfafa fatan shiga tattaunawa kai tsaye da Isra´ila.


Shirya wannan taro kaɗai wata nasara ta diplomasiyya ga shugaban na Syria Bashar al-Assad da kuma yadda ƙasashen duniya ke kimanta Syria bayan ta daɗe a matsayin saniyar ware a duniya. Shugaban Faransa Nikolas Sarkozy ke wakiltar ƙungiyar EU sannan Sheikh Hamad al-Kalifa na Qatar a matsayin wakilin majalisar ƙasashen yankin Golf sai Assad kansa a matsayin shugaban ƙungiyar kasashen Larabawa. Shi kuwa firaministan Turkiya Tayyip Erdogan shi ne jagora a tattaunawar farfaɗo da shirin zaman lafiya tsakanin Syria da Isra´ila. Kawo yanzu Turkiya ta jagoranci zaman tattaunawa har sau huɗu tsakanin ƙasashen maƙwabtan juna waɗanda a hukumance suke cikin yaƙi. To sai dai a gun taron an samu labari maras daɗi dake cewa an ɗage zagaye na biyar na tattaunawar sakamakon murabus da babban mai shiga tsakani na Isra´ila Yoram Turbowicz ya yi. Amma duk da haka Assad ba da tabbacin cewa zaman lafiya da Isra´ila shi ke kan gaba a ajandar Syria.


Ya ce "Da mu da Isra´ila mun gabatar da shawarwari. Ta nuna aniyar janyewa daga Tuddan Golan saboda haka ana iya ganawa kai tsaye. Amirka za ta taka muhimmiyar rawa a nan amma fa ƙarƙashin sabuwar gwamnatin Washington. Ba bu tababa dangane da rawar gani da Turkiya ke takawa bisa manufa. Burinmu shi ne mu saka Faransa a cikin tattaunawar , amma dole mu jira mu ga abin da zai faru a Isra´ila nan gaba."


Tun bayan isar Sarkozy jiya a Damascus shugaba Assad ya fito fili ya nuna masa cewa kawo yanzu suna tattauanawa da Isra´ila bisa shiga tsakanin Turkiya a matsayin wani mataki na amincewa da juna.

Taron wanda aka fara a cikin Mayu ya bawa Assad wata dama ta shiga nahiyar Turai. Wani dalilin da ya sa Sarkozy ya gayyaci Assad zuwa birnin Paris shi ne cewa shugaban na Syria na taka muhimmiyar rawa kuma mai ma´ana wajen ƙauracewa shiga wani yaƙin basasa a Lebanon. Bugu da ƙari kuma Assad na ɗasawa da shugabannin Iran, inda wataƙila zai sa ya shawo kansu a samu wata masalaha dangane da shirinta na nukiliya da suke taƙadama da kasashen yamma. Assad dai ya nuna shirin ba da haɗin kai a gun taron na yaau.

Ya ce "Mun tattauna wannan batu da shugaba Sarkozy. Fatan mu shi en warware wannan rikici cikin lumana. Za mu ci-gaba da tuntuɓar juna da Faransa sannan za mu riƙa shaidawa Iran abubuwan da muka tattauna."

Tun a ganawar da suka yi jiya shugaban na Syria ya faɗawa Sarkozy cewa duk wani hari da za a kaiwa Iran zai haddasa wani mummunan sakamako. Assad ya kuma nuna damuwa game da halin da ake ciki Lebanon yace idan Syria ta fara tattaunawa kai tsaye da isra´ila to ana yia shigar da Lebanon ciki. Ya ce za a samu narasa ne kaiwa idan aka samu wani ci-gaba mai ma´ana game da batun Falasɗinawa.