1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron tattalin arzikin duniya ba wasu jiga-jigai

Yusuf Bala Nayaya
January 21, 2019

Shirye-shiryen fara taron kasuwancin na duniya na shekara-shekara ya kankama daga Talata zuwa Jumm'a a birnin Davos na kasar Switzerland yayin da ake samun karin kalubalen tattalin arziki da duniya ke fuskanta.

https://p.dw.com/p/3Bu7G
Logo Weltwirtschaftsforum, World Economic Forum, WEF
Hoto: picture-alliance/dpa/J.-C. Bott

Taron tattalin arziki na duniya yana zuwa lokacin da ake rasa bunkasa tattalin arzikin duniya, ga rikicin kasuwanci da ake samu gami da matsalolin da suka dabaibaye muhalli wadanda aka gaza warwarewa a lokaci guda ga sauyi da ake samu na mayar da lamura zuwa na zamani. Klaus Schwab yana cikin wadanda suka kirkiro taron wanda ya nuna muhimmancin ci gaban tattaunawa batutuwan "Tattaunawa domin samun fahimtar juna, ya zama dole fiye da kowanne lokaci."

A gaba daya ana sa ran shugabannin gwamnatoci 70 da na Majalisar Dinkin Duniya gami da hukumomin kudi na kasashen duniya za su kasance cikin wakilai kimanin 3,000 da za su halarci taron. Bugu da kari akwai kimanin ministoci 300 da shugabannin kamfanoni 1000 da masana kimiyya. Borge Brende tsohon ministan harkokin wajen Norway ke shugabancin taron na tattalin arziki na duniya:

Norwegen Der Aussenminister Borge Brende
Borge Brende tsohon ministan harkokin wajen NorwayHoto: Getty Images/AFP/A. Kisbenedek

"Kalubalen yanzu shi ne shugabannin gwamnatocin kasashe da za su halarci taron, 'yan kasuwa da 'yan kungiyoyi masu zaman kansu domin matsa lamba bisa muhimman batutuwa da duniya ke fuskanta."

Shugaba Donald Trump na Amirka wanda ya yi kaurin suna kan watsi da yarjejeniya tsakanin kasashen duniya ba zai halarci zaman taron bana ba, saboda takaddamar da ta janyo rufe harkokin gwamnatin Amirka.

Haka Shugaba Emmanuel Macron na Faransa saboda ayyukan sun yi masa yawa, amma a zahiri saboda taron na masu hannu da shuni ka iya dagula tattaunawa da 'yan kasa da yake yi. Sai dai Shugabar gwamnatin Jamsu Angela Merkel da Annegret Kramp-Karrenbauer wadda za ta gaje ta kan shugabancin jam'iyyar CDU mai mulki za su halarci taron tare da ministan kiwon lafiya Jens Spahn. Sabon Shugaba Jair Bolsonaro na Brazil zai bayar da jawabin farko na kasa da kasa lokacin zaman taron na Davos. Bolsonaro ya yi kaurin suna bisa batun nuna kishin kasa. Duk da yake babu saka hannu kan wata yarjejeniyar yayin taron na Davos amma rashin Shugaba Donald Trump na Amirka zai rage armashin taron da ke daukar hankali.

Schneechaos in den Alpen - Davos
Za a halarci taron a yanayin dusar kankaraHoto: Reuters/A. Wiegmann

Taron zai duba ci-gaba mai daurewa da ya kunshin duk bangarorin al'umma. Kana kason wakilcin mata ya kasance kashi 22 cikin 100, inda aka samu kari daga kashi 21 cikin 100 a shekarar da ta gabata.