1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron AU ya amince da muhimman matakan ci gaba

Suleiman Babayo
January 29, 2018

Taron shugabannin kasashen Afirka da aka kammala a birnin Addis Ababa na kasar Habasha ya amince da wasu matakai kan inganta sufurin jirage gami matakin inganta kasuwanci da hadewar jama'a.

https://p.dw.com/p/2rj3d
Äthiopien Addis Abeba Afrikanische Union Gipfel
Shugabannin kasashen Afirka a taron Addis Ababa na kasar HabashaHoto: picture-alliance/AA/M. W. Hailu

Shugabannin kasashen Afirka da suka kammala taro a birnin Addis Ababa na kasar Habasha sun amince da wasu muhimman matakan inganta sufurin jiragen sama gami da matakin inganta kasuwanci da ma hadewar al'umar nahiyar. Bayan taron ma yini biyu, ya kuma sami amincewar babban sakatare na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres wanda ya ce yana goyon bayan duk wani matakin da kasashen na Afirka suka dauka game magance rikice-rikice da ake samu a nahiyar musamman a Sudan ta Kudu da aka bayar da wa'adi ga bangarorin da suke hana ruwa gudu bisa rikicin kasar. 

Äthiopien Addis Abeba Afrikanische Union Gipfel Guterres
Sakatare Janar na MDD, Antonio GeterresHoto: Reuters/T. Negeri

Guterres, ya ce "akwai rikice-rikice da dama wadanda aka tura dakarun kiyaye zaman lafiya, amma ba a dauki matakan magance matsalar ba. Manufamu ita ce sake tattauna hanyoyin kiyaye zaman lafiya a kasashen Sudan ta Kudu da Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

 

Antonio Guterres ya kuma nuna muhimmancin aiki tare tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar ta Tarayyar Afirka AU, kan magance rikice-rikice da barakar siyasa da ake samu a wasu kasashen nahiyar.

Fiye da shugabannin kasashe da gwamnatoci 40 ne suka halarci taron na birnin Addis Ababa. Shugaba Paul Kagame na Ruwanda ya dauki shugabancin karba-karba na kungiyar kuma ya nuna muhimmancin samun kasuwanci da sufuri na bai daya tsakanin nahiyar abin da ya janyo kaddamar da shirin sufurin jiragen sama na bai dayan da tsarin kasuwanci na nahiyar, kamar yadda Shugaba Kagame ya yi karin haske.

Ruanda vor den Wahlen 2017
Shugaba Paul Kagame na kasar RuwandaHoto: Imago/Zumapress/M. Brochstein

Ya ce "kaddamar da tsarin sufurin jiragen sama na bai daya a nahiyar Afirka, wannan shirin gagarumin mataki ne na sufuri gami da tsarin ciniki na nahiyar"

Matakin zai taimaka wajen rage tsadar sufurin jiragen sama a nahiyar inda ake da tsari mafi tsada idan aka kwatanta da sauran nahiyoyi. Daga cikin kasashe 55 mambobin kungiyar Tarayyar Afirka, tuni 23 suka saka hannu kan daftarin samar da tsarin kasuwanci. Wani abin da ya dauki hankali lokacin taron na kwanaki biyu, shi ne hanyoyin aiki tare tsakanin kasashen Afirka domin yaki da cin hanci wanda ke zagon kasa ga tattalin arzikin kasashen.

Wani lamarin kuma da taron ya bukaci a kara himmatuwa a kai shi ne hanyar kara hade mutanen nahiyar a matsayin al'umma guda ta fannonin rayuwa da aiki tare. Duk suna cikin tsarin samar da bunkasa da zaman lafiya mai dorewa a nahiyar zuwa shekara ta 2063.