1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron duba ɗimamar yanayi a birnin Bonn na Jamus

August 6, 2010

An kammala taron duba canjin yanayi a Jamus ba tare da cimma matsaya ba

https://p.dw.com/p/OeHP
Christiana Figueres, shugabar ofishin MƊD akan canjin yanayiHoto: DW

Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) ta kawo ƙarshen tattaunawa akan matsalar yanayi a birnin Bonn ba tare da cimma wata matsaya ba. Wannan taro an gudanar da shi wata huɗu kafin shiga wanni babban taro a ƙasar Mexico. A taron na yini biyar mahalarta daga ƙasashe daban-daban sun tattauna akan sabon rahoto akan matsalar canjin yanayi, ko da yake wasu ƙasashen sun nuna rashin amincewa da ci-gaban da aka samu a tattaunawar da aka yi a watan Disamba bara a birnin Copenhagen na ƙasar Denmak. A dai birnin na Copanhagen ƙasashen su tsai da shawarar samar da dala miliyan dubu ɗari a kowace shekara kafin shekarar 2020 domin kauce wa abin da ka iya haifuwa daga matsalar ɗimamar yanayi da kuma tanadar da dala miliyan dubu goma kafin shekarar 2012. An dai bayyana shakku game da cimma wannan manufa. An kuma samu ƙaruwar shafukan da rahoton ya ƙunsa daga 17 zuwa 34. Sabuwar shugabar shirin Majalisar Ɗinkin Duniya akan ɗimamar yanayi, Christiana Figueres ta ce ya zamo wajibi a dakatar da ci-gaban wannan rahoto.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Mohammad Nasiru Awal