1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

G20: Duniya ta himmatu kan yaki da sauyin yanayi

Abdoulaye Mamane Amadou
October 31, 2021

Gwamnatoci da shugabannin kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 sun cimma daidaito kan manufa daya ta rage dumamar yanayi da maki daya da rabi

https://p.dw.com/p/42P98
Italien Rom | G20 Gipfel | Münzwurf am Trevi Brunnen
Hoto: Jeff J Mitchell/Getty Images

Shugabannin kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya G20 sun cimma matsaya guda ta kawo karshen hayaki mai gurbata muhalli daga yanzu zuwa tsakiyar wannan karnin da muke ciki.

Shugabannin sun baiyana hakan ne a karshen taron koli na kwanaki biyu da suka kammala a birnin Rome na kasar Italiya domin cimma matsayar da za su gabatar a babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi a birnin Glasgow na yankin Scotland.

Firaministan Italiya Mario Draghi ya shaidawa shugabannin cewa suna bukatar daukar matakai na dogon zango da kuma na wucin gadi domin cimma muradun da suka sanya a gaba.

A sanarwar bayan taro da suka fitar shugabannin kasashen na G20 sun yanke hukuncin dakatar da gina sabbin tashoshin samar da wutar lantarki da ke aiki da gawayi daga karshen wannan shekara, sai dai hakan ba ya nufin cewa za a dakatar da aiki da gawayin a cikin kasashe da suka hada da China da India.