1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron G7 ya watse baram-baram a kanada

Mouhamadou Awal Balarabe
June 10, 2018

Shugaba Donald Trump ya yi watsi da sanarwar bayan taron shugabannin kasashe bakwai da suka fi karfin tattalin arziki a duniya bayan da mai masaukin baki Justin Trudeau na Kanada ya soki tsarin kasuwancin Amirka.

https://p.dw.com/p/2zE68
Kanada G7 Gipfel Abreise Donald Trump
Hoto: Reuters/J. Ernst

Cikin wani sakon Tweeter ta ya wallafa a kan hanyarsa ta zuwa Singapor, Trump ya soki Firaminisran Kanada Justin Trudeau kan caccakar Amirka da ya yi dangane da sabon kudin fito da ta kakaba kan karfe da aluminim, inda ya dangantashi da mai rashin gasakiya da karfin fada a ji.

Wannan sakon na Trump ya zo ne sa'o'i kalilan bayan gama taron shugabannin G7 wanda ya kasa cimma matsaya a kan kasuwanci sakamakon takaddamar da ke tsakaninsu kan lamura da dama. Dama dai Shugaba Trump ya bar taron tun gabanin a gama shi, inda ya nanata maganar da yayi cewa kawayen Amirka na kwararta a fagen cinikayya. Sannan ya nuna wajibcin sake dawo da kasar Rasha a matsayin memba, ko da shi ke ministan harkokin wajen kasar Sergei Lavrov ya ce a kai kasuwa.