1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron girmamawa ga marigayi Helmut Kohl

Salissou Boukari
July 1, 2017

A wannan Asabar din ce daya ga watan Yuli, kungiyar Tarayyar Turai ke gudanar da gagarumin taron girmamawa ga tsohon shugaban Gwamnatin Jamus Helmut Kohl, da ya rasu a ranar 16 ga watan Yuni.

https://p.dw.com/p/2fkL2
Straßburg Trauerfeier Europa nimmt Abschied von Helmut Kohl
Gawar tsohon shugaban Gwamnatin Jamus Helmut KohlHoto: Reuters/A. Wiegmann

 Wannan biki na ta'aziyya zai gudana ne a majalisar Tarayyar Turai da ke birnin Strasbourg, inda ake sa ran halartar tawagar shugabanni fiye da 40, sannan kuma mafi yawan shugabannin Tarayyar Turai za su samu halartar wannan biki na ta'aziyyar. Firaministar Britaniya Theresa May ta tabbatar da halartar bikin, sannan kasar Amirka ta aiko da tsohon shugaban kasar Bill Clinton sai kuma tawagar kasar Rasha za ta zo ne a karkashin jagorancin Firaminista Dmitri Medvedev. Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da shugaban kasar Ukraine  Petro Porochenko za su kasance daga cikin masu halartar taron ta'aziyyar da Tarayyar Turai ta shirya.

Tsohon shugaban gwamnatin ta Jamus daga shekara ta 1982 zuwa 1998 Kohl ya taka rawar gani wajen hadewar kasar ta Jamus a matsayin kasa daya da kuma cigaban Tarayyar Turai. Za a dauki gawarsa bayan bikin ya zuwa birnin Speyer a nan Jamus, inda za a yi  jana'izar sa. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana marigayi Helmut Kohl da kasancewa babbar sa'a da Jamus ta taba samu, mutumin da ake kira jagoran hadin kasan kasar. A wata ganawa da ta yi da Paparoma Fransis, Merkel ta ce jagoran na darikar Katolika na duniya ya mika mata sakonsa na ta'aziyya.