1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kafafen yada labaru na Global Media Forum na 2016

Mohammad Nasiru AwalJune 16, 2016

A bana taron na Global Media Forum da tashar DW ke daukar bakoncinsa a kowace shekara ya duba yanayin aikin jarida a fasahar digital da 'yanci da kyawawan dabi'u.

https://p.dw.com/p/1J89j
Bonn Global Media Forum GMF 01 | Opening Ceremony
Hoto: DW/K. Danetzki

Taron na Global Media Forum ya samu halartar kasashe 100 daga sassa dabam-dabam na duniya, taron na tsawon kwanaki uku ya gudana daga 13 ga wannan wata na Yuni zuwa 15 ga wata.
Taken taron na bana dai shi ne: "Kafafen sadarwa, 'Yanci, Kyawawan Dabi'u", kuma an tattauna batutuwa da dama ciki kuwa har da na kare 'yancin dan Adam da kuma rawar da kafafen yada labarai ka iya takawa wajen yaki da cin zarafin mata da kananan yara.