1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kasa da kasa kan 'yan gudun hijira a Jamus

Yusuf Ibrahim/YBJuly 12, 2016

Majalisar Dinkin Duniya dai ta bayyana cewar sama da mutane miliyan 65 ne suka kaurace wa muhallansu mafi akasari yara da mata.

https://p.dw.com/p/1JNdj
Deutschland Steinmeier mit Teilnehmern der Flüchtlingskonferenz in Berlin
Ministan harkokin wajen Jamus Steinmeier a tsakiya lokacin taron 'yan gudun hijira a BerlinHoto: picture-alliance/dpa/R. Jensen

Wakilai daga kungiyoyin agaji na kasa da kasa sun taru a birnin Berlin na kasar Jamus karkashin bakuncin ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier domin tattaunawa kan kalubalen da 'yan gudun hijira ke fiskanta a duniya.Majalisar Dinkin Duniya dai ta bayyana cewar sama da mutane miliyan 65 ne suka kaurace wa muhallansu mafi akasari yara da mata.Mahalarta taron sun fito ne daga kungiyoyi kamar ta kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR, da kungiyar kasa da kasa mai kula da 'yan gudun hijira ta (IOM) da kungiyar agaji ta Red Cross.Peter Sutherland, shi ne wakili na musamman na sakataren Majalisar Dinkin Duniya kan harkokin 'yan gudun hijira, a wajen taron na Berlin ya bayyana matsalar 'yan gudun hijira da sakaci na kasa da kasa:

"Samun matsala wajen daukar nauyi da ya rataya a wuyanmu kan batun na 'yan gudun hijira shi ne dalili da ya sanya Fafaroma Francis lokacin da yake barin birnin Istanbul a jirginsa ya dauko 'yan gudun hijira fiye da yadda wasu kasashe 21 na Kungiyar EU suka dauka daga Siriya. Wannan abin kunya ne garemu."