1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kolin Afirka da Turai

Umaru AliyuDecember 6, 2007

Shirye-shiryen taron kolin kasashen Afirka da na kungiyar hadin kan Turai a Lisbon

https://p.dw.com/p/CYTY
Shugaban Zimbabwe Robert MugabeHoto: AP

A yan kwanakin nan babu wani abin dake daukar hankali, a shirye-shiryen taron kolin ƙasashen Afirka da na Turai, in banda Robert Mugabe. Har ma wasu sun fara ƙorafin cewar shirye-shiryen taron zasu tattara ne kawai a game da ko shugaban na Zimbabwe zai halarci taron ƙolin na Lisbon a ƙarshen wannan mako, ko da shike akwai al’amura da dama da ya kamata a duba a shawarwarin na ranar takwas da tara ga watan Disamba. Akwai batun haɗin kann tattalin arziki da kwararar yan Afirka zuwa Turai da aiyukan kiyaye zaman lafiya ƙasashen Afirka, misali a yankin Darfur.

A bayan makomar Mugabe a zauren taron kolin na Lisbon, tsakanin ƙasashen Afirka da na ƙungiyar hadin kann Turai, wata matsalar kuma da ta addabi masu shirya taron, shine yada zasu saukar da manyan baƙi da zasu halarce shi. Shugaban Libya, Muammar Gaddafi alal misali, yace ba zai yarda a sauke shi a gagarumin Hotel mai tsada ba, amma a maimakon haka, yafi so ne a samar masa da tanti da ya dace inda zai zauna. Haka nan suma sauran yan tawagar dake yiwa Gaddafi rakiya, kimanin dari biyu, cikin su har da mata dake tsaron lafiyar sa, wajibi ne a samar masu da tanti inda zasu zauna.

Sai dai masu ɗaukar nauyin shirya taron ƙolin na Portugal, sun kasa samun nasarar shawo kan wata matsalar dabam. Wannan matsala kuwa ita ce ta kasancewar shugaban ƙasar Zimbabwe, Robert Mugabe a zauren taron. A sakamakon matakan keta haƙƙin yan Adam a Zimbabwe, ƙungiyar hadin kann Turai ta dora takunkumi kann gwamnatin ta Mugabe. Sakamakon haka, sabon Pirayim ministan Ingila, Gordon Brown a watan Satumba yace ba zai halarci taron ƙolin na Lisbon ba, muddin Robert Mugabe zai kasance a wurin taron.

Yace wannan dai taron ƙoli ne mai muhimmanci ga matakan kyautatawa nahiyar Afrika. Babu shakka kasancewa ta a zauren taron,, idan a lokaci guda shugaba Mugabe shima ya halarci taron, abu ne ko kaɗan ba zai dace ba, kuma akwai alamun Mugabe yana da niyyar halartar taron.

A bayan wnanan jawabi ne aka shiga kai da komo n diplomasiya. Da farko shugabannin Portugal sun nuna sun fi kaunar ganin Gordon Brown a zauren taron ƙolin, amma ba Mugabe ba, to amma ƙasashen Afrika da dama suka yi barazanar cewar idan har ba a gaiyaci Mugabe ba, suma ba zasu shiga taron ba. Ta wannan hanya, dukkanin shugabannin ƙasashen ƙungiyar tattalin arziki ta kudancin Afrika, wato SADC suka nuna goyon bayan su ga Robert Mugabe, cikin su har da shugaban Mozambique, Armando Guebuza.

A ra’ayi na, wajibi ne mu hada tawagar da zata wakilce mu da kanmu. Daya nahiyar bai kamata a ƙyale ta zaɓar mana waɗanda zasu wakilce mu ba. Zamu tafi da tawagar da muka zaɓa tayi magana da Turai.

Ita ma shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, wadda zata wakilci ƙasar ta a Lisbon ta goyi bayan Mugabe ya halarcci wannan taron ƙoli.

Tun da farko Jamus ta dauki matsayin cewar wajibi ne a gaiyaci dukkanin ƙasashen ƙungiyar haɗin kann Afrika, inda ko wacce daga cikin wadannan ƙasashe ya rage gareta ta zaɓi waɗanda zasu wakilce ta. Hakan kuwa yana nufin zamu faɗi ra’ayoyin mu, zamu yi suka inda ya dace muyi suka, amma sai idan waɗanda za’a yi domin su suna nan. Dukkan su gaba ɗaya kuwa suna da yancin halartar wannan taro.

Pirayim ministan Portugal, Jose Socrates yace an tsara al’amura da dama da za’a tattauna kansu. Za’a duba batun tafiyar da mulki na-gari a Afrika da batun canje-canje na yanayin sararin samaniya da kuma kwararar yan Afirka zuwa nahiyar Turai.

ƙololuwar taron kolin dai an shirya zai kasance sanya hannu ne da za a yi kann yarjejeniyar yancin cinikaiya tare da ƙasashe da dama na Afirka. To amma wannan bangare tilas a dakatar dashi, saboda har yanzu ba a sami nasarar kammala shawarwari da ƙungiyoyin tattalin arzki dabam dabam na yankunan Afirka ba tukuna. Babban abin dake hana ruwa gudu, shine kiran da kungiyar hadin kann Turai ta yi wa Afirka domin ta kara bude kasuwannin ta ga kayaiyakin ƙasashen ƙungiyar haɗin kan Turai.