1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron komitin sulhu akan Darfur

Zainab A MohammadAugust 29, 2006
https://p.dw.com/p/BtyT
Kofi Annan na MDD da Alpha Omar Konare na AU
Kofi Annan na MDD da Alpha Omar Konare na AUHoto: AP

An gudanar da taron sirri tsakanin wakilan komitin sulhun mdd,dake fuskantar rarrabuwar kawuna dangane rikicin Darfur din kasar Sudan.

Wannan taro yazo ne adaidai lokacin da Amurka ke cigaba da zargin Sin adangane da kawo cikas akokarin da ake na tura rundunar kiyaye zaman lafiya a yankin yammacin kasar dake fama da rigingimu.

Taron wakilai 15 na komitin dai yazo ne adaidai lokacin da Sudan tayi watsi da matsin lambar da ke mata na amincewa da daftarin kudurin Amurkan da Britania ,wanda ke bukatar a tura ayarin dakarun kiyaye zaman lafiya akarkashin jagorancin mdd a lardin darfur.

Kudurin na tura dakaru dubu 17 a karkashin mdd,na nufin maye gurbin na kasashen Afrika da ahalin yanzu ke sudan din ,kuma ke fama da karancin kayayyakin aiki,wadanda kuma kawo yanzu sun gaza shawo kann kashe kashen rayuka da fyade wa mata ,da matsaloli na kauracewa da fararen hula keyi,domin tsira da rayukansu.Jakadar Amurka a Jendayi Frazer,wadda takai ziyarar neman hadin kann gwamnatin sudan din a khartum,na shirin barin kasar ba tare da cimma bukatu ba,sai dai kawai wasika daga shugaba Hassan Omar Al-Bashir,inda yake jaddadawa shugaba Bush adawarsa da tura dakarun kiyaye zaman lafiya a kasarsa.

Adangane da halin da Darfur din ke ciki kuwa,Mataimakin sakatare general na Mdd Mark Malloch Brown ya jaddada cewa"yace yana da matukar muhimmanci mu mayar da hankali kann Darfur,saboda akwai ababai munana dake gudana a wannan lardin".

A taron na jiya dai,manyan jamian mdd dake kula da harkokin agaji sun fadawa komitin sulhun halin da ake ciki a yanzu a lardin Darfur.

Theo Mrphy daga kungiyar kare hakkin jamaa ta kasa da kasa yace halin da ake ciki a Darfur abun ban tausayi da takaici"Mutanen dake sansanonin gudun hijira bayan asaran matsunnensu har yanzu suna fuskantar hare hare ,ayayinda ake cigaba dayiwa mata fyade,a wasu lokuta ma akayi musu azabar dakan haddasa mutuwa".

A wata wasikar da aka gabatar a makon daya gabata dai,shugaba Omar Al-Bashir na Sudan din ,yayi kira ga wakilan komitin dasuyi taka tsantsan a dangane da Darfur,tare da gardinsu dangane zartar da kuduri cikin gaggawa akan darfur din.Ya kuma bukace su dasu bar gwamnatinsa ta warware matsalarta ,tare da bata daman aiwatar da yarjejeniyar sulhu da aka cimma,ta hanyar tallafawa dakarun Afrikan da kayayyakin aiki.

Jakadan Sudan a mdd Omar Bashir Mohammed Manis yace"ban ga dalilin da zaisa zaa tura dakarun soji,zuwa cikin kasar da tace bata marabtan wadannan sojojin ba"

Shi kuwa jakadan kungiyar kasashen larabawa Yanah Mahmassani cewa yayi"Tura dakarun kiyaye zaman lafiya zuwa sudan,ba tare da amincewar gwamnatin Khartum ba,zai dada haifar da matsala fiye da wadda ake da ita yanzu".

A shekara ta 2003 nedai lardin Darfur ya fada wannan rikici daya kawo yanzu ,yaki ci yaki cinyewa tsakanin bakaken fata larabawa marasa rinjaye da gwamnatin Khartum,wadda ke nuna musu wariya wajen cin moriyar kaddarorin kasa.