1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kula da harkokin tsaro na Munich

February 2, 2013

Taron na ƙasa da ƙasa zai mayar da hankali ne a kan rikice rikice da ake fama da su a Mali da kuma Syriya.

https://p.dw.com/p/17Wvs
eft, Egypt's Foreign Minister Mohamed K. Amr, second from left, publisher Josef Joffe, right, U.S. Senator Joseph I. Lieberman, second from right, and Tunisia's Prime Minister Hamadi Jebali talk during a panel discussion at the Conference on Security Policy on Sunday, Feb. 5, 2012 in Munich, Germany. Politicians and military representatives gathered for the Munich Security Conference that began Friday, Feb. 3. (Foto:Frank Augstein/AP/dapd)
Hoto: AP

Bayan kasashe dake samun bunkasa yanzu, kamar  Brazil da Chna, suma kasashen Afrika suna daga cikin  wakilai 400 daga kasashe fiye da 70 da  zasu halarci tzaron na Munich tun daga  daya zuwa uku ga watan  Fabrairu masu bunkasa. Tuni kuma, wannan taro ya zama  ba matattara ta yan siyasa bane kadai.  Suma masana tattalin arziki da wakilan kungiyoyi masu zaman kansu sukan hahllara domin shiga tattaunawar da akan yi.  Hakan dai ya maida taron tsaron na birnin Munich a matsayin wani  dandali na  nazari da kuma duba canbje-canjen al'amuran  tsaro a duniya baki daya a karni na 21, inda bayan  batun  tsaro da yadda za'a fuskanci  sabon zamani na  yaki ta amfani da yanar gizo,  za'a kuma yi nazarin batun  canjin yanayin sararin samaniya.

 Taron zai kuma tattauna batun kasuwanci tsakanin ƙaasahen

start of the 49th Conference on Security Policy, in Munich February 1, 2013. World leaders including U.S. Vice President Joe Biden, NATO Secretary General Anders Fogh Rasmussen and Spain's Foreign Minister Jose Manuel Garcia-Margallo are due to participate in the security conference on Sunday. REUTERS/Michaela Rehle (GERMANY - Tags: POLITICS)
Sicherheitskonferenz München SicherheitsvorkehrungenHoto: Reuters

Duk kuma da taruka masu yawa da ake amma ana ci gaba da samun karuwar massu bukatar halartar  tarojn na tsaro a Munich. Wakilai dabam dabam har kimanin 90 ne zasu hallara a zauren taron. Tawagar da babu shakka zata fi daukar hankali ita ce  wadda mataimakin shugaban Amerika, Joe Biden yake wa jagoranci. Mataimakin shugabanna Amerika  ya taba halartar taron na Munich a shekara ta 2009,  inda ya gudanarda  jawabi a game da dangantakar dake tsakanin Amerika da Rasha. Tun kafin ya isa birnin na Munich sai da Biden ya yada zango a Berlin, inda ya gana da shugaban gwamnati, Angela Merkel. Daga baya, ta shaidawa manema labarai cewa:

Mun tattauna a game da batun daidaita al'amuran kasuwannin hada hadar kudi na duniya, mun tattauna a game da al'amuranda suka shafi  manyan kasashen duniya bakwai masu karfin tattalin arziki da   rukunin kasashe ashirin masu ci gaba, muna kuma aiki tare da hadin kai kan  manufofinmu na tsaro, musamman a game da yakin da muke yi a Afghanistan da kuma yaki da aiyukan tarzoma a duniya baki daya.

Ziyarar da  mataimakin shugaban na Amerika, Joe Biden ya kai Berlin, jim kadan bayan da aka rantsar dashi karo na biyu kan wnanan mkami, wata alama ce ta kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Bayan al'amura na siyasa da tsaro, shugaban gwamnati, Angela Merkel da ministanta na harkokin waje, Guido Westerwelle  ysun dade suna kokarin ganin an sami wata yarjejeniya ta ciniki da kawar da  fito a kayaiyakin da kasashen suke sayarwa junan su. Shi  kansa a lokacin wannan ziyara Joe Biden ya kwatanta Jamus a matsayin kawa kuma abokiyar hadin gwiwa ta hakika.

Manyan kalubalan da ke a gaban taron sune na tabbatar da zaman lafiya

Auf dem Bild: Übersicht auf der Münchener Sicherheitskonferenz München 1.2.2013 Foto: Rosalia Romaniec / DW
Hoto: DW/R.Romaniec

Jamus kasa ce  da zata ci gaba da kasancewa mai matukar muhimmanci a dangantaka tsakanin kasashen Turai da Amerika, kuma kasar da ta zama tushen da muka dora dangantakar su da sauran duniya baki daya a  kansa, wanda kjma idan ba tareda nahiyar Turai mai karfi ba, yana da wuya mu iya hangen yadda dangantakar Amerika zata kasance da sauran duniya.

A wannan shekara, karon farko,  daga cikin masu halartar taron na Munich har akwai ministan harkokin wajen Brazil da kuma babban mai gabatar da  masu laifi a kotun kasa da kasa a  birnin Hague. Manyan al'amuran da taron  na bana zai  maida hankali kansu, sun hada har da  rikice-rikicen da ake fama dfasu a Mali da Syria da kuma yadda  za'a yi da Iran.

Mawallafi : Umaru Aliyu

Edita        : Usman Shehu Usman