1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kungiyar G-8 a St. Petersburg

July 15, 2006
https://p.dw.com/p/BuqV

A yau ake fara taron kolin kungiyar kasashe mafiya arzikin masana´antu a duniya G-8 a birnin St. Petersburg na Rasha. Rikicin yankin GTT zai mamaye ajandar taron. Ana sa ran cewa kasashen kungiyar ta G-8 zasu samar da matsayi na bai daya akan rikicin na GTT. Bugu da kari zasu kuma tattauna game da shirin nukiliyar Iran kana kuma zasu bukaci KTA ta dakatar da gwajin makamai masu linzami. Babban jigon taron na yini 3 dai shine tabbatar da samar da makamashi a duniya baki daya.