1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kungiyar kasashen musulmi(OIC)

Hauwa Abubakar AjejeSeptember 13, 2006

Mahalarta taron kungiyar kasashen musulmi ta duniya sunyi kira ga manyan attajiran musulmi da su sayi hannuwan jari na manyan kafofin yada labarai na duniya,domin taimaka kawadda kyamar addinnin da wasu suke nunawa.

https://p.dw.com/p/BtyB
Tutar kungiyar
Tutar kungiyar

Ministoci da manyan jamiai dake taro karkashin kungiya mafi girma ta musulmi wato OIC,sunce an shafawa musulunci bakin fenti,tun bayan harin 11 ga watan satumba,wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane kusan 3,000,wanda aka dora laifinsa akan wasu larabawa 19.

Shugaban kungiyar ta musulimi Ekmeleddin Ihsanoglu ya fadawa mahalarta taron a garin Jeddah,cewa dole ne masu saka jari na kasashen musulmi su sayi hannayen jari na manyan kafofin yada labaran na duniya,domin su samu damar sa baki cikin manufofinsu,ko tsare tsarensu.

Yace yin hakan zai taimaka wajen sake farfado da martabar addinin musulunci a idanun jamaar koina cikin duniya.

Yana mai kara yin kira ga kasashen musulmi da su kakkafa kafofin yada labarai da zasu rika yada labarai na manyan harsuna na duniya.

Ya zuwa yanzu dai,musulmi basu da jari mai karfi cikin manyan kafofin yada labari,inda aka nuna cewa,yarima Al Waleed na Saudiya ne kadai yake da hannun jari kashi 5 da kusan rabi kacal cikin gamaiyar kanfanonin Rupert Mudock da kafar yada labarai ta Amurka Fox ke karkashinsa.

Musulmi da dama dai suna ganin cewa martani da Amurka tayi dangane da harin na ranar 11 ga watan satumba,ta hanyar mamayar Iraqi da Afghanistan tare da dakile yancin farar hula a ciki da wajen kasarta,yaki net a kaddamar akan musulunci.

Hakazalika batun zana hoton batunci da akayiwa manzon Allah(SAW),shima ya kara munana rarrabuwar kawuna tsakanin musulmi da aladar yammacin duniya.

Ministan yada labarai na kasar Masar,Anas Al faki,wajen taron ya baiyana cewa,yadda aka tasowa addinin musulunci shekaru biyar da suka shige,wato bayan harin na Amurka,ya tilastawa musulmi su kare addinin tare da fadakar da jamaa game da yadda addinin yake.

Yace yanzu fiye da kowane lokaci,musulmi suna bukatar yin anfani da kafofin yada labarai domin yada kyakkyawar akidar musulunci a dukkan sassa na duniya,yana mai bada misali da yakin kwanaki 34 da Israila ta kaddamar akan Lebanon,a matsayin wani batu daya kamata musulmi suke bukatar baiyana raayinsu da yadda abubuwa suka gudana.

Idan dai baa manta ba kasar saudiya ta taba yin gargadi game da kuskure da akeyi wajen danganta taaddanci ga wani addini ko kabila daban.

Tare kuma da irin illar dake tattare da nuna son kai ko banbancin launin fata,da sunan yaki da taadanci.