1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kungiyar tsaro ta NATO

Suleiman Babayo
July 12, 2018

Shugaban Amirka Donald Trump ya nunar da cewa a fahimtarsa kasashen kungiyar tsaro ta NATO sun amince da kara kudaden tsaro da suke kashewa lokacin taron kungiyar da ke gudana a birnin Brussels na kasar Beljiyam.

https://p.dw.com/p/31L4Z
Belgien Brüssel Pressekonferenz Donald Trump
Hoto: picture-alliance/AP Photo/G. Vanden Wijngaert

Tun farko Shugaba Trump ya yi barazanar cewa Amirka za ta yi gaban kanta kan lamuran tsaronta, sannan ya zargi Jamus da zama 'yar amshin Shata na Rasha saboda yadda take samun makamashi daga Rashar, abin da ya janyo martani mai zafi daga hukumomin Jamus.

Sannan Shugabar gwamnatin ta Jamus ta nuna muhimmanci bambance batun tsaro da kasuwanci maimakon hada komai a faifai guda da shugaban na Amirka ke yi. Shi dai Shubaga Trump ya ce yanzu kungiyar ta NATO tana da karfi fiye da 'yan shekarun da suka gabata. Wani abu kuma da aka gabatar lokacin taron shi ne an gayyaci kasar Macedoniya a hukumance ta shiga cikin kungiyar ta NATO.

Belgien EU NATO Donald Tusk, Jens Stoltenberg und Jean-Claude Juncker
Hoto: picture-alliance/AP Photo/G. V. Wijngaert

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya yi nuni da rashin samun wata tangarda musamman daga shugaban Amirka kamar yadda wasu ke tunani cikin bayanin da Macron ya yi ga manema labarai a wannan Alhamis.

 

Xavier Bettel Firamnistan Luxembourg ya nuna muhimmancin tattauanwa da kasar Rasha, daya daga cikin wadanda ake gani tana takun saka da wasu kasashe musamman na gabashin turai da ke cikin kungiyar ta NATO.

Bisa manufa kasashen da ke kungiyar tsaron ta NATO ya dace su kashe kimanin kashi biyu cikin 100 na kudaden shiga kan harkokin tsaro, kuma abin da Shugaba Donald Trump na Amirka ke fata kenan zuwa shekara ta 2019. A wannan Alhamis ake kawo karshen taron na shugabannin kasashen na kungiyar tsaron ta NATO.