1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin gida na KTT a Brussels

December 1, 2005

Ministocin cikin gida na kasashen KTT sun gudanar da taronsu a Brussels yau alhamis

https://p.dw.com/p/Bu3l

A dai halin da ake ciki yanzun kasashen Turai sun fara tunanin kafa wata runduna ta hadin guiwa tsakaninsu domin tsaron iyakokinsu na gabar tekun baharum domin dakatar da tuttudowar bakin haure, kamar yadda aka ji daga zauren taron ministocin cikin gida na kasashen Kungiyar tarayyar Turai a brussels yau alhamis. An saurara daga bakin kantoman hukumar zartaswa ta KTT akan al’amuran shari’a Franco Frattini yana mai ba da shawarar cewa mai yiwuwa nan gaba kasashen arewacin Afurka, kamarsu Libiya, Tunesiya, Aljeriya da Maroko, wadanda ta kansu ne ‚yan gudun hijirar suka saba bi domin karasowa zuwa Turai, su shiga a rika damawa da su a matakin sintirin domin tsaron iyakokin dake tsakaninsu a gabar tekun baharurum. Kazalika bisa ga ra’ayin Farattini wajibi ne a samar da wasu ka’idoji bai daya tsakanin kasashen KTT dangane da karbar baki ‚yan kaka-gida domin ta haka ne kawai za a iya karya alkadarin ‚yan baranda dake fatacin dan-Adam da satar hanyar shigowa da bakin haure zuwa nahiyar Turai. Frattini ya ce:

A zamanin baya kasashen kungiyar tarayyar Turai sun bayyana kyamar danka alhakin lamarin a hannu kafofin hukumar zartaswa ta kungiyar. Amma a yanzu sai ga shi suna alla-alla su ga hakan ta samu domin bin wata manufa bai daya tsakaninsu.

A nasa bangaren sabon ministan cikin gida na Jamus Wolfgang Schäuble baya goyan bayan wannan ra’ayi na Frattini, inda ya fito fili ya ce ba KTT ce zata yanke hukunci a game da ko wane ne ke da ikon neman kaka-gida a Jamus ba.

Na bayyana ra’ayina a game da gaskiyar cewa ba hukumar zartaswa ta KTT ce ke da alhakin yanke hukunci a game mutanen dake da ikon neman kaka-gida a nahiyar Turai ba. Wannan matsala ce da ta danganci matsayin kasuwar kodago a kowace kasar da lamarin ya shafa kuma a saboda haka hukumominta ne kadai ke da damar yanke wannan hukunci.

Shi dai Schäuble, a ganinsa, abu mafi alheri shi ne kungiyar tarayyar Turai ta mayar da hankalinta wajen yaki da bakin haure. Ba zata yiwu a zauna sasakai a zura na mujiya ana kallon yadda rayukan mutane ke salwanta a tekun baharrum a kokarinsu na neman tsallakowa zuwa Turai ba. A baya ga tsauraran matakai na tsaron iyaka, nan gaba akwai bukatar hadin kai da kasashe matalauta da wadannan ‚yan gudun hijira suka fito domin magance matsalar dake haddasa guje-gujen hijirar daga tushenta. Muhimmin abin da wadannan mutane ke bukata shi ne wata kyakkyawar makoma ga rayuwarsu ta yau da kullum a kasashensu. A lokacin taron nasu dai ministocin na cikin gida na kasashen KTT sun albarkaci wani rahoton kungiyar akan yaki ta’addanci. Rahoton yayi nuni da kyakkyawan hadin kai da aka samu a tsakanin kasashen kungiyar akan wannan manufa a cikin watanni 18 da suka wuce.