1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin harkokin wajen EU akan makomar lardin Kosovo

September 8, 2007
https://p.dw.com/p/BuC4

Ministocin harkokin wajen kasashen KTT 27 na wani taro a kusa da birnin Porto na kasar Portugal a wani mataki na cimma matsaya guda a dangane da makomar lardin Kosovo dake cikin Sabiya. Wasu daga cikin kasashen kungiyar EU na goyon bayan shawarar da MDD ta bayar na bawa lardin mai rinjayen kabilar Albaniyawa ´yancin kai daga Sabiya. To sai dai gwamnati a birnin Belgrade ta ce ba zata taba yarda ta saki wannan yanki don radin kanta ba. Kungiyar EU da kasashen Rasha da Amirka ke jagorantar jerin tattaunawar da ke gudana tsakanin sassan biyu da nufin cimma wani daidaito kafin karshen wannan shekara. Ministan harkokin wajen Jamus F.-W. Steinmeier ya yi fatan cimma tudun dafawa bisa manufa.

Steinmeier:

“Ina tabbatar da cewa damar da muke da ita kadan ce, amma duk da haka zamu yi kokari mu ci-gaba da jagorantar da tattaunaawar tsakanin Sabiya da Kosovo don fadada wannan dama.”