1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin kudin kasashen kungiyar G-8 a Mosko

February 11, 2006
https://p.dw.com/p/Bv8Y

An bude taron ministocin kudi na kungiyar G8 ta kasashen da suka fi arzikin masana´antu a duniya a birnin Mosko. Taron dai wanda a karon farko Rasha ke karbar bakoncinsa zai fi mayar da hankali ne akan batun samar da makamashi a duniya baki daya. Hakazalika taron zai share fagen taron kolin da kungiyar ta G8 zata yi a birnin St. Petersburg a cikin watan yuni mai zuwa. Kamfanonin dillancin labarai sun rawaito cewa taron share fage na ministocin kudi ya nuna goyon baya ga aniyar Rasha ta biyan basussukan da kasashen kungiyar Paris Club ke binta kan kari. Bugu da kari ministocin sun yi maraba da shirin da gwamnati a birnin Mosko ta nuna na kara yawan taimakon da take ba kasashe masu tasowa sakamakon rarar ciniki da ta ke samu a fannin makamashi.