1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU Entwicklungshilfeminister

October 22, 2010

Nagartattun hanyoyin da za a bi wajen amfani da kuɗaɗen taimakon

https://p.dw.com/p/PlfJ
Hoto: AP

Duk da matsaloli na bashi da matakan tsuke bakin aljihu da ƙasashen yammaci ke fama da shi, amma fa maganar watsi da manufofin raya ƙasashe masu tasowa ba ta ma taso ba. Muhimmin abu shi ne nagartattun hanyoyin da za a bi wajen amfani da kuɗaɗen taimakon. Akan haka ministocin taimakon raya ƙasashe masu tasowa na ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai suka gudanar da taronsu a birnin Brussels.

A sakamakon matsalolinsu na kasafin kuɗin ƙasa, gwamnatocin ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai na fama da wahala wajen yi wa al'umarsu cikakken bayani a game da dalilinsu na ci gaba da ba da taimakon raya ƙasa ga ƙasashe masu tasowa. Sai dai kuma ministan taimakon raya ƙasashe masu tasowa na ƙasar Belgium Charles Michel ya ce maganar ba ta shafi gabatar da kuɗaɗen taimako ne ko ta halin ƙaƙa ba.

"Taimakon raya ƙasa ba wani alheri ne ake yi wa ƙasashe masu tasowa don samun kwanciyar hankali ba. Magana ce da ta shafi maslahar dukkan waɗanda lamarin ya shafa. Abu ne da ya danganci kyautata makomar rayuwar ɗan-Adam baki ɗaya."

A nasa ɓangaren ministan taimakon raya ƙasashe masu tasowa na Jamus Dirk Niebel bai yi irin wannan jawabi na wuce gona da iri ba. A ra'ayinsa kawo yanzu ana gabatar da taimakon ne ba tare da ba da la'akari da yadda ake aiwatar da su ba.

"Wajibi ne taimakon ya duƙufa akan sakamakon da zai iya samarwa. Wajibi ne mu riƙa tunani a game da tasirin taimakon da muke bayarwa, amma ba yawan kuɗaɗen taimakon ba. A baya ga haka wajibi ne ƙasashen dake samun taimakon su ƙara yin hoɓɓasa wajen ɗaukar ƙaddararsu a hannunsu. Domin kuwa mu kanmu ba zamu iya samarda ci gaba ga wata ƙasa ba, wannan alhaki ne da ya rataya a wuyan gwamnatocin kasashen a wawware. Wannan shi ne babban sharaɗin da ya kamata mu ba wa goyan baya."

Sai dai kuma duk da haka Niebel na goyan bayan ganin an ƙara yawan kuɗaɗen da ƙungiyar tarayyar Turai ke kashewa a manufofin ƙetare da na tsaro da kuma taimakon raya ƙasashe masu tasowa. Bisa ga ra'ayinsa dukkan waɗannan manufofi guda uku suna da dangantaka da juna. In da so samu ne da zai so ya ga an ƙayyade kuɗaɗen da ƙungiyar ke kashewa wajen karya farashin amfanin noma. Kuma wani abin dake ci wa Niebel tuwo a ƙwarya a manufofin taimakon raya ƙasashe masu tasowa na ƙungiyar tarayyar Turai kuma shi ne irin banbance-banbancen dake akwai tsakanin su kansu ƙasashe a ma'amallarsu da ƙasashe masu tasowa.

Jamus dai na daga cikin rukunin ƙasashen da suka kasa cimma burin Majalisar Ɗinkin Duniya na bunƙasa yawan kuɗaɗen taimakon zuwa kashi sufuli da ɗigo bakwai cikin ɗari na jumullar abin da ƙasar ke samarwa. Wasu ƙasashen ƙungiyar ma dai daɗa tsuke bakin aljihunsu suke yi game da kuɗaɗen taimakon sakamakon matsalolin tattalin arziƙi. Amma kantoman ƙungiyar tarayyar Turai akan taimakon raya ƙasashe masu tasowa na da ra'ayin cewar hakan ba ta isa zama dalili ba.

"A matsayinmu na hukumar zartaswa ta ƙungiyar tarayyar turai zamu ci gaba da matsin lamba domin ganin ƙasashe ba su ƙayyade yawan taimakonsu ba."

Illahirin ƙasashen ƙungiyar dai sun ci alwashin ɗaga yawan taimakonsu zuwa kashi sufuli da ɗigo bakwai cikin ɗari aƙalla nan da shekara ta 2015.

Mawallafiya: Ahmad Tijani Lawal