1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron shugabannin kasashen larabawa

March 29, 2007
https://p.dw.com/p/BuOq

Shugaba Mahmoud Abbas na yankin Palasdinawa yayi gargadin dangane da cigaban tashe tashen hankula a wannan yankin idan har Izraela bata bata amince da tayin sulhu ta aka mika mata ba.Inda yayi kira dangane da bukatar gudanar da taron kasa da kasa wajen cimma wannan buri na zaman lafiya a yankin.ayayu nedai akesaran shugabannin kasashen larabawa zasu bada amincewarsu ta karshe adangane da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Izraela da palasdinu.A karshen wannan taro nasu na yini biyu a birnin Riyadh din kasar saudi Arabia,anasaran shugabannin kasashen yankin gabas ta tsakiyan zasu bukaci Izraela data amince da wannan yarjejeniya,wadda aka fara gabatar da ita shekaru 5 da suka gabata.Tuni Izraelan tayi watsi da muhimman batutuwa dake kunshe acikin wannan yarjejeniya,wadanda suka hadar da maido da yankuna da suka mamaye kann iyaka gabannin 1967.