1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron yaki da ta'addanci a birnin Abuja

September 3, 2014

A ci-gaba da kokarin daura damarar yaki da masu tayar da kayar baya, ministocin harkokin wajen kasashen duniya sun gudanar da wani taro a babban birnin Tarayyar Najeriya.

https://p.dw.com/p/1D65e
Nigeria Boko Haram Chris Olukolade Militär PK 12. Mai
Hoto: picture alliance/AP Photo

Kama daga bara da ke cikin jihar Yobe kuma sabuwar amaryar daular Boko Haram ya zuwa Bama da Banki da Kawuri da ma Gamborun Ngala da Gwoza da ke zaman sabuwar cibiyarta dai, sannu a hankali dai tana kara fari da yin kanshi ga 'ya'yan kungiyar da ke ci-gaba da kame garuruwa ba wahala, sannan kuma ke kara nuna irin jan aikin da ke gaban mahukuntan Najeriya da ke tsakiyar yaki na ta'adda.

Barazanar kuma da ta dauki hankalin Ministocin harkokin wajen kasashen Faransa da Birtaniyya da Kamaru da mai masaukin bakin ta Najeriya sannan da wakilai daga China da Amirka da Niger da kuma Tarrayar Turai da ma 'yar uwanta da ke yankin yammacin Africa wato ECOWAS game kuma da kungiyar kasashen musulmin OIC da suka share wunin ranar Laraba suna nazarin ci gaban yaki da ta'addancin tun bayan tarukan biranen Paris da Washington a 'yan watannin baya.

Shiru na alkawarin da aka dauka

Nigeria Armee Anschlag in Abuja 25.6.2014
Hoto: REUTERS

A baya dai wadannan kasashen na zaman na kan gaba a cikin alkawarin taimaka wa Tarrayar Najeriya ganin karshen matsalar da ke ta da hankula sannan kuma ke barazanar mai da sashen arewa maso gabashin kasar tunga ta masu aikin na ta'addanci zalla.

To sai dai kuma daga dukkan alamu taron na Abuja ya kai ya zuwa karshe ba tare da wani sabon sauyi na azo a gani a bisa matakan da ke akwai tun farko ba. Matakan kuma da daga dukkan alamu suka kai ga karya sojan kasar maimakon kara musu karfi na ganin karshen yakin da ya sauya daga na sunkuru sannan kuma ya koma na zomo da kare a tsakanin 'yan kungiyar da ke farautar soja a halin yanzu.

Ambassador Aminu Wali dai na zaman ministan harkokin wajen Najeriya wanda ya ce hakuri na zaman wajibi a bangaren 'yan kasar da ke kallon gazawa a bangaren mahukuntan kasar da ke jagorantar yakin.

“Ya kamata a sani cewar yaki irin na 'yan ta'adda ba irin ragowar yakin da aka sani ba ne. Su 'yan ta'adda sai sun zabi lokaci da wurin da suke so suje inda babu kowa. Ba za ka iya cin nasarar yakin nan ba har sai ka samu hadin kan kasashen da ke kewaye da mu da wadanda suka zo domin taimaka mana. Nasarar yaki na tare da sanin sirrin mutanen da kake yaki da su, wadanda kuma suka zo suna da hanyoyi daban-daban na samun sirri na mutanen da ke yakin da mu. Mun kuma samu fahimtar juna cewar za mu rika samun kyakyawan labari kan irin abubuwan da suke ciki yadda zai bamu damar fahimtar abun da suke kokarin yi kafin su zo yadda za mu samu nasara a kansu.”

A baya dai irin wannan alkawarin Turawan ya gaza kaiwa ga ceto 'yan mata na Chibok da suka share kusan watanninsu biyar a dokar daji duk da agaji da dabarun 'yan yamman.

Ana dai kallon rikon sakainar kashi da halin ko in kular mahukuntar da zama musabbabin kazancewar matsalar da ta sauya daga dan haki ta koma allura a gaban idanun 'yan mulkin na Abuja.

Siyasa da rayukan mutane

Flüchtlingslager in Bama, Nigeria
Sansanin 'yan gudun hijira a BamaHoto: Reuters/S.Ini

To sai dai koma wace dabara ta rage ga Abujar da masu bukata na taimaka matan dai can a cikin yankin, siyasa ce ke neman kunno kai a cikin yankin a tsakanin gwamnatin Jihar Borno da ke fadin har yanzu gari na biyu mafi girma a jihar wato Bama na hannun soja da kuma wakilin yankin a majalisar dattawan Najeriya kuma dan gari Senata Ahmed Zanna da ya ce tuni karkarar tasu ta yi nisa a cikin bi ga sabuwar daular yankin.

“Yaran Boko Haram sun shiga Bama sun dauki Bama kuma sojoji sun gudu an kuma kashe mutane ba kadan ba. Ina mamaki da jihar ke kokarin yin siyasa da rayukan mutane, wannan ba abun siyasa ba ne. Kudaden da suke ci bai ishe su ba sai sun yi siyasa da rayukan mutane, wannan bai dace ba. Ni din nan daga Bama nake.”

Rahotannin da ke fitowa daga rundunar sojan kasar dai na nuna kara tura tankokin yaki ya zuwa yankin da nufin tunkarar yakin da ya rikide daga dan sunkuru ya zuwa na gwajin karfi a tsakanin 'yan tsaron da masu takama da sabuwar daular tasu.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal