1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron yan majalisar APF a Libreville

Yahouza S.MadobiJuly 6, 2007

Yan majalisar dokokin ƙasashe masu anfani da halshen faransanci sun gudanar da taro a birnin Libreville

https://p.dw.com/p/Btv6

Majalisar Dokokin APF ta ƙunshi wakilan majalisun dokoki daga ƙasashe fiye da 40, masu anfani da halshen faransanci a dunia.

A wannan karo yan majalisa fiye 250 su ka halarci taron wanda shine zama na 33 da ƙungiyar APF ta yi.

Mahimman batutuwa da su ka tantana sun haɗa da matsalolin baƙin haure, dake kwarara daga ƙasashen Afrika renan Fransa, zuwa nahiyar turai.

An gudanar da wannan mahaura tare da halartar ministan Fransa mai kula da baƙin haure Brice Hortefeux, wada ta issar da saƙon shugaban ƙasar France, Nikolas Sarkozy a game da manufofin sa, na magane matsalolin baƙin haure.

Nikolas Sarkozy, ya yi ƙaurin suna a nahiyar Afrika,a game da tsautsauran matakai da ya ɗauka na yaƙi da baƙin haure.

A jawabin da yayi an bude taron shugaban ƙungiyar ƙasashen masu anfani da faranci Abdu Diouf, ya bayyana kyaukyawar rawar da yan majalisar APF ke takawa ta fannin kauda rigingimu a ƙasashen dunia.

Abdou Diouf yayi anfani da wannan dama inda ya gabatar da ayyukan da hukumar sa ta ƙaddamar, ta fannin ƙara haɗin kai tsakanin ƙasashen ƙungiyar OIF.

Taron na 33 ya yi daidai da cikwan shekaru 40 da kafa wannan ƙungiya, bisa shawara tsofan shugaban ƙasar Senegas, Leopold Sedar Senghor.

Mahalarta taron Libreville sun gudanar da mahaura, a game da rikita-rikitar da ke wakana a wasu ƙasashe membobin APF.

Sun maida hankali mussamnam, a kan halin da ake ciki a ƙasashen Libanon, Cote D´Ivoire, Tchad, da Jamhuriya Afrika ta tsakiya.

Yan majalisar dokokin APF, sun yaba ingantacen ci gaba da ka samu, a ƙasar Mauritania da Jamhuriya Demkoradiyar Kongo, bayan zaɓɓuɓukan demokarɗiya tsabttatu da aka shirya a ƙasashen 2.

Gabanin wannan zaɓe, yan majalisar APF, sun fida Mauritania, da Jamhuriya demokradiyar Kongo, daga ƙungiyar, a sakamakon abinda su ka ta kira take haƙƙoƙin tsarin mulkin demokradiya.