1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe tashen hankula a Iraki a rana ta farko ta azumin ramadana

September 23, 2006
https://p.dw.com/p/BuiQ

A rana ta farko da fara azumin watan ramadana an kai wani mummunan harin bam a unguwar Sadr City ta ´yan shi´a dake wajen birnin Bagadaza. Akalla mutane 34 suka rasu sannan fiye da 30 suka samu raunuka a fashewar wani bam da aka dana cikin mota a kusa da wani gidan mai. Wata kungiya da ta kira kanta jama´atul Jundal Sahaba ta yi ikirarin kai harin. Rundunar sojin Iraqi ta yi gargadi game da karuwar kai hare hare a Iraqi cikin watan azumin na ramadana. A kuma can garin Muktadiya dake arewa da birnin Bagadaza, jami´an tsaro sun kame madugun kungiyar Ansar al-Sunna, da ake zargi da kai hare haren ta´addanci a fadin kasar Iraqi.