1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe-tashen hankula a wasu kasashen Afirka

Mohammad Nasiru AwalJanuary 23, 2015

Rikicin Boko Haram da tashe-tashen hankula a Nijar da kuma bore a Janhuriyar Demokradiyyar Kwango suka mamaye labarun jaridun na Jamus a kan nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/1EPWI
Kamerunische Soldaten an der Grenze zu Nigeria Archiv 12.11.2014
Hoto: AFP/Getty Images/R. Kaze

A labarinta mai taken Boko Haram na barazana ga kasashe makwabtan Najeriya jaridar Berliner Zeitung ta fara da cewa baya ga Najeriya yanzu kasar Kamaru na kara zama wani filin daga ga 'yan ta'addan na Boko Haram. Jaridar ta ce a farkon mako kungiyar ta kai hare-hare a kan wasu kauyuka da ke jihar arewa mai nesa ta kasar Kamaru, inda ta yi garkuwa da mutane da yawa ciki har da 'yan mata da samari kimanin 50 masu shekarun haihuwa tsakanin 10 zuwa 15. Daga bisani rundunar sojin Kamaru ta ce bayan wata mummunar musayar wuta da masu tsattsauran ra'ayin, ta ceto mutane kimanin 20 daga cikin wadanda Boko Haram ta yi garkuwa da su. Ganin yadda kungiyar ta addabi yankin, kasar Chadi ta tura dubban sojoji zuwa Kamaru don yakar kungiyar. Jaridar ta ci gaba da cewa a jamhuriyar Nijar ma an ga alamun bullar Boko Haram, inda a lokacin zanga-zangar nan ta karshen makon jiya an ga wasu dauke da tutocin kungiyar.

An ceto Bajamushe daga hannun Boko Haram

Ita kuwa jarida Bild Zeitung ta mayar da hankali ne a kan sakin Bajamushen nan wanda ya kwashe tsawon watanni shida a hannun Boko Haram. Ta ce a cikin watan Yulin shekarar 2014 mayakan kungiyar suka sace malamin Bajamushe daga jihar Adamawa zuwa wani wuri inda suka yi barazanar fille masa kai. To amma wata rundunar soji ta musamman a Kamaru ta ceto Bajamushen. Sai dai jaridar ta ce ba a yi karin bayani kan yadda aka ceto shi ba, amma yana cikin koshin lafiya.

Mummunar zanga-zanga a Nijar

Niger Anti Charlie Hebdo Protest Islam Koran 17.01.2015
Hoto: Reuters/T.Djibo

A lokacin da take tsokaci kan boren da aka yi karshen mako a jamhuriyar Nijar jaridar Neue Zürcher Zeitung ta bayyana hakan da wata rana mai cike da bakin ciki a Nijar. Ta ce a karshen mako an gudanar da jerin zanga-zanga a kasashe da yawa don yin tir da mujallar Charlie Hebdo ta kasar Faransa, amma zanga-zanga mafi muni ta auku ne a Nijar, musamman a birnin Yamai fadar gwamnati da kuma Zinder. Baya ga rayuka da suka salwanta an yi kuma kone-kone har da majami'u da yawa. Jaridar ta kara da cewa irin wannan zanga-zanga na daukar sabon salo a kasashen Afirka kudu da Sahara, inda wasu kungiyoyi ke amfani da halin da ake ciki suna kokarin sanya gaba tsakanin mabiya addinai da kabilu dabam-dabam da suka shafe shekaru aru-aru suna zaman lafiya da juna.

Asarar rayuka a Kwango a boren adawa da Kabila

Kongo Unruhen in Kinshasa
Hoto: Reuters/N'Kengo

Zakin mulki inji jaridar Süddeutsche Zeitung tana mai cewa shugaban jamhuriyar Demokradiyyar Kwango Joseph Kabila yana da niyar yin tazarce, matakin da ya haddasa mummunan boren da ya yi sanadin mutuwar mutane. Ta ce kundin tsarin mulkin kasar ya ba wa shugaban kasar wa'adin mulki sau biyu a jere bayan nan dole Kabila ya sauka a badi. Amma gwamnatinsa ta gabatar wa majalisar dokoki wani kudurin doka da ya tanadi kidayar 'yan kasa a matsayin sharadin shirya sabon zabe. Amma a kasa kamar Kwango za a dauki shekaru da yawa kafin a kammala kidayar al'ummarta. Abin da ka iya sa a jinkirta zaben abin da kuma zai ba wa Kabila damar ci gaba da mulki.