1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashin bama-bamai sun ruɗa birnin Alƙahira

January 24, 2014

A kasar Masar an samu fashewar wasu ababai da ake kyautata zaton bam ne a gaban hedkwatar rundunar 'yan sandan da kuma a tashar jiragen ƙasa a babban birnin ƙasar.

https://p.dw.com/p/1AwR3
Kairo Anschlag 24.01.2014
Hoto: picture-alliance/dpa

Fashewar abin wanda ya faru da sanyin safiyar yau ya hallaka mutane hudu a oshin yan sandan, kana a tashar jiragen ƙasa mutun guda ya mutu wasu kimanin 15 suka jikkata, kamar yadda gidan talabijin din kasar ya shaida. Kana fashewa ta uku ta auku ne a kusa da wurin yawon bude ido na birnin, wanda ƙasar Masar ke matuƙar gadara da shi.

Kazalika rahotanni na cewar wasu 'yan bindiga sun bude wuta kan ginin da aka kai harin jim kadan bayan fashewar abin.

Ya zuwa yanzu dai ba a tantance masu hannu a wannan lamari ba wanda 'yan sandan Masar din ke cewar na kama da hari na kunar bakin wake.

Wannan dai na zuwa ne kwana guda kafin a cika shekaru uku da yin juyin-juya halin kasar Masar din wanda ya yi awon gaba da gwamnati shugaba Hosni Mubarak.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman