1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar nazari da bincike a littattafai

April 23, 2019

Hukumar Raya Ilimi da Al'adu ta Malajisar Dinkin Duniya UNESCO ta ware ranar 23 ga watan Afirilu a matsayin ranar littattafai ta duniya da kuma yaki da satar fasaha.

https://p.dw.com/p/3HIJk
Symbolbild Weiterbildung Beruf
Muhimmanci littattafai ga dalibaiHoto: Fotolia/Africa Studio

Bincike ya nunar da cewar dalibai a Tarayyar Najeriya sun yi watsi da karatun sababbin littattafan da marubuta ke wallafawa, daidai lokacin da kasashen da suka ci-gaba suka rungumi kafafen sadarwa na zamani a matsayin hanyoyin karatu. Tun dai a shekara ta 1995 ne hukumar ta UNESCO ta fara gudanar da wannan biki na ranar littatafan. Sai dai a Najeriya duk da cewa kusan ko wace shekara a kan samu sabon littafi da aka wallafa da ke da nasaba da bincike kama daga na makarantun sakanddare zuwa na gaba da ssakandaren, sai dai ba kasafai dalibai ke amfani da su ba. Wasu dalibai da DW ta tattauna da su sun tabbatar da cewa a yanzu suna amfani da wayoyinsu na salula ko kuma na'urar computer wajen gudanar da bincikensu. Sai dai masana na ganin cewa hakan na janyo koma baya wajen samun bincike da kuma kirkire-kirkire da dalibai suka gudanar da kansu, kasancewar mafi akasari suna amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen yin nazari da ma bincike.