1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin rediyo tsakanin al'umma

February 13, 2013

Ranar daukaka martabar gidajan rediyo dangane da rawar da suke takawa wajen inganta rayuwar al'umma da ci gaban kasashe.

https://p.dw.com/p/17dhS
Welttag des Radios, englisch: World Radio Day, kurz: Weltradiotag am 13. Februar Retro radio © Serggod - #32877444 - Fotolia.com
Hoto: Fotolia/Serggod

Ranar 13 ga watan Fabrairu ita ce ranar rediyo ta duniya wacce hukumar raya ilimi da bunkasa al'adu ta Maljalisar Dinkin Duniya wato UNESCO ta kaddamar a karo na farko a shekarar bana a wani mataki na neman daukaka martabar gidajan rediyo dangane da rawar da suke takawa wajan inganta rayuwar al'umma da ci gaban kasashe.

Jamhuriyar Nijar na daga cikin kasashen Afirka da ta kunshi gidajan rediyo masu yawa tsakanin masu zaman kansu na gwamnati da ma na raya karkara. Aikin rediyo dai yana tasirin a kasar kana al'umma da gwamnatin kasar suna yaba aikin nasa.
Ko baya ga gidajan rediyo sama da 200 da ke da akwai a kasa kamar Nijar, kasa na daya daga cikin daya dayar kasashen nahiyar Afirka da ake sauraran shirye shiryen  manyan gidajan rediyoyi na duniya irinsu DW, BBC, RFI, VOA, RADIO CHINA, RADIO TEHERAN kai tsaye ta hanyar karamin zango na FM, kuma al'adar sauran rediyo al'ada ce da ta jima a tsakanin al'ummar kasar ta Nijar inda kusan babu wani mutum a birnin ko kauye da bai mallaki akwatin rediyo ba domin sauraran labaran duniya da sauran shirye shiryen.

Rediyo na taka rawa wajen ilmantarwa

Albarkacin wanann rana ta rediyo ta duniya wakilinmu a Yamai Gazali Abdou Tasawa ya ji ra'ayin wasu ma'abota sauraran rediyo a birnin Yamai dangane da yadda suke kallon aikin radiyoyi, inda dukkannensu suka jaddada muhimmancin sauraron shirye shiryen gidajan rediyo musamman don sanin halin da duniya ke ciki da kuma samun karin ilimi. Alhaji Amada Bashar dake zama dan jaridar Hausa na farko a Nijar ya taka rawa a cikin aikin rediyo a kasar da ma sauran kasashen duniya.

Logo unseres Partnersenders Radio Dunyaa FM in Dakar (Senegal)
Radio Dunyaa FM a Dakar na daya daga cikin tashoshin dake hulda da DW

Kafa rediyo don raya karkara

Albarkacin wanann rana ta rediyo ta duniya gwamnatin Nijar ta gudanar da wani biki na kafa wani gidan rediyo a wani kauye mai suna Kahe na kusa da birnin Yamai inda kuma ya bayyana kaddamar da wani shiri da zai mayar da hankali ga inganta aikin gidajan rediyon raya karkara ta hanyar samar masu da wadataccen kayan aiki kamar dai yadda ministan sadarwa na Nijar Malam Isaka Boucher ya nunar.
 

Ranar 13 ga watan Fabrairu na shekara ta 1946 ne Majalisar Dinkin
Duniya ta bude gidan rediyonta, abunda ya sanya hukumar ta UNESCO ta
kaddamar da wannan rana a matsayin ta rediyo a duniya.

***Fotos nur für den Artikel " Einblicke" verwenden*** DW Mitarbeiter Peter Hille
DW na da miliyoyin masu sauraro a AfirkaHoto: DW

Yanzu haka dai duk da matsalolin da gidajan rediyo suke fuskanta a Nijar da ma wasu kasashen Afirka, bai hana su kasance a sahun gaban hanyoyin samar da ayyukan yi ga matasa ba.

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Mohammad Nasiru Awal