1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin yakin Siriya ga Turai

December 5, 2013

Turai ta koka game da barazanar da yakin Siriya ke yi ga tsaron nahiyar.

https://p.dw.com/p/1ATtd
Syrien Kämpfe 27.08.2013
Hoto: Reuters/Ammar Abdullah

Kasashen Faransa da Beljiam sun yi kashedi game da cewar, karuwar matasa 'yan kasashen Turai da ke tallafa wa mayakan 'yan tawayen da ke da alaka da kungiyar alqa'ida, wadanda kuma ke neman kifar da gwamnatin shugaba Assad na siriya, wata babbar barazana ce ga sha'anin tsaron nahiyar Turai. Ministan kula da harkokin cikin gidan Faransa Manuel Valls, wanda yayi jawabi ga menama labarai daura da takwaran aikinsa na Beljiam Joelle Milquet sun bayyana cewar, matsalar tana da tada hankali sosai, musamman yadda take tsananta. A yanzun nan da ake batu dai, matasan da yawansu ya kama daga 1,500 zuwa 2,000 daga nahiyar Turai suka garzaya zuwa Siriya domin shiga a dama dasu a fafutukar da 'yan tawaye ke yi na kifar da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad.

Daga Beljiam dai, a cewar minista Milquet, akwai tsakanin mayaka 100 zuwa 150, yayin da Valls kuwa ya ce kimanin Faransawa 400 suka je Siriya, inda 180 ke can kuma suna fafatawa har i zuwa wannan lokacin, kana 14 sun mutu, yayin da wasu 80 kuma tuni suka koma gida Faransa. Ya kuma ce akwai wasu 100 da ke son barin kasar ta Siriya domin dawowa Faransa.

A dai baya bayan nan ne wata makarantar kwaleji a birnin London na Birtaniya wato King's College, ta kiyasta cewar, kimanin Turawa 600 ne suka tafi Siriya domin gwabza yaki, tun bayan rikicin da ya barke daga shekara ta 2011.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Pinado Abdu Waba