1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawa kan matsalar tsaro a Najeriya

October 23, 2014

A ci gaba da kokarin mafita ga annobar rashin tsaron da ke kara barazana ga Tarayyar Najeriya

https://p.dw.com/p/1DbG6
Hoto: imago/Wolf P. Prange

Sannu a hankali dai ido na da budewa, sannu a hankali kuma ana kara fahimtar lamura a cikin yaki da ta'addancin Tarayyar Najeriya da ke cikin shekararsa ta biyar da kuma ke ci gaba da daukar hankali ciki dama wajen kasar.

Zaman hadin gwiwa tsakanin cibiyar Fredrisch Ebert mai helkwata a kasar Jamus da kungiyar kwararru kan harkoki na kasa da kasa suka ce matsalar ta'ddancin kasar ta Najeriya na da ruwa da tsaki da watsi da kyautata rayuwar mazauna iyakokin kasar dama na kasashen da ke fama da annobar ta ta'ddanci.

Masana daban-daban cikin kasar ne dai suka kai ga tsokaci ga halin rashin kular da a cewarsu ya rikide ya zuwa rikicin ta'addancin da ya addabi kowa a kasar.

Duk da cewar dai ra'ayi ya kai ga rabewa a bisa girman banbancin da ke akwai a tsakanin irin girman matsalolin da ya kai matasa irin nasu Bama da Baga kai wa ga rungumar akidar Boko Haram, a fadar Farfesa Anthony Asiwaju da ke zaman wani kwarraren masani bisa rayuwar mazauna kan iyakokin kasar ta Najeria:

Symbolbild Gewalt in Nigeria
Hoto: SEYLLOU DIALLO/AFP/Getty Images

“Shin ka taba zuwa yankin ? Ni na taba, kuma in fada maka wurin da kake magana na zaman babban alama ta rashin kulawa da kuma tsabar talauci, saboda kawai suna kan iyaka."

Nazari kan hali na rayuwar mazaunan na iyaka dai na zaman wani sabon yunkuri na sauyin salo daga karfi na tuwo ya zuwa sabbabin dabaru na kyautata rayuwar al'umma. A fadar shugaban kungiyar masanan harkoki na kasa da kasa Farfesa Nuhu Omeiza Yakubu da ke kallon adalci a zaman mafita ga ta'addanci a ko'ina cikin kasar da ke fuskantar zabe a badi.

To sai dai yayin da ake maganar sabbin dabarun tuni ta dai bayyana Shugaban kasar Goodluck Ebele Jonathan na shirin shiga fage da nufin yankar takardar sake tsayawa takarar shugaban kasar a zabuka.

Nigerias Terror geht weiter
Hoto: DW/K. Gänsler

Shugaban ya kaddamar da wani kwamitin da zai jagoranci takarar tasa a wani taron da ya gudanar a tsakaninsa da wasu zabbabin gwamnonin jam'iyyar da ragowar makarrabansa a fadar gwamnatin kasar ta Aso rock a Abuja. Karkashin jagorancin tsohon ministan tsaron kasar Dr Bello Halliru Mohammed kwamitin na da mutane 36 da aka dora wa alhakin tsara kaddamar da takarar ta Jonathan.