1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawa ta zama dole a rikicin Siriya

December 29, 2012

Waɗannan su ne kallamun da wakilin MDD a Siriya Lakhdar Brahimi ya yi a birnin Mosko inda ya gana da Sergei Lavrov

https://p.dw.com/p/17BCp
U.N.-Arab League peace mediator Lakhdar Brahimi (L) of Algeria and Russia's Foreign Minister Sergei Lavrov attend a joint news conference in Moscow December 29, 2012. The international mediator seeking to end the 21-month-old conflict in Syria met Russia's foreign minister in Moscow on Saturday after talks in Damascus but expectations of progress toward a negotiated solution were low. REUTERS/Sergei Karpukhin (RUSSIA - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Manzon masammun na Malalisar Ɗinkin Duniya a ƙasar Siriya Lakdar Brahimi da ministan harkokin waje na ƙasar Rasha Sergei Lavrov su dukanin su sun yi amanar cewar bin hanyoyin diflomasiya su ka ɗai  ne zasu iya kai ga warware rikicin Siriyar.

Da ya ke yi magana a birnin Mosko a ƙarshen wasu taruruka da ya gudanar da babban jami'n diflomasiyar na ƙasar Rasha Lakdar Brahimi ya ce Siriya na shirin fuskantar wani bala'i idan ba a samu sulhu ba a tashin hankali.Ya ce ''ita hanya kai ɗai  hanya ko a fuskanci mumunar bala'i ko kuma a bi hanyoyin neman sulhu ya ce abin na da wahala da sarƙaƙiya amma ba mu da zaɓi.Ministan harkokin waje na ƙasar Rasha Sergej Lavrov ya ce ba babban kuskure ya ce dole sai shugaba Bashar Assad ya sauka daga mulki maimakon tattaunawa.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita       : Mahamadou Awal Balarabe