1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawa tsakanin jami'an Jamus da Najeriya

October 20, 2014

Ministan harkokin wajen Jamus zai gana da na Najeriya yayin taron 'yan kasuwa a birnin Berlin

https://p.dw.com/p/1DYuv
Hoto: AFP/Getty Images/Emmanuel Dunand

A gobe Talata aka shirya ganawa tsakanin ministan harkokin wajen kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier da takwaransa na Najeriya Aminu Bashir Wali. Yayin ganawar bangarorin da su tattauna kan dangantakar kasashen biyu.

Tattaunawar tsakanin jami'an kasashen za ta mayar da hankali kan harkokin siyasa, da kasuwanci, da makamashi da al'adu da kuma shige da fice.

Ministan harkokin wajen na Najeriya Aminu Bashir Wali yana birnin Berlin na kasar ta Jamus inda ake tattaunawa ta kasuwanci tsakanin 'yan kasuwan Afirka da na Jamus, kuma a gefen tattaunawar ne za a yi ganawar tsakanin Wani da kuma ministan harkokin wajen Jamus Steinmeier.

A wannan Litinin Hukumar Lafiya ta Duniya ta tabbatar da cewa an samu nasarra kawar da cutar Ebola daga Tarayyar Najeriya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu Waba