1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawar ƙawayen Siriya

June 22, 2013

Ministocin harkokin waje na ƙasashe 11 na ƙoƙarin samar da han'yo'yin taimaka wa 'yan tawayen Siriya da makamai a taron da suke yi a ƙasar Qatar.

https://p.dw.com/p/18uT1
U.S. Secretary of State John Kerry (R) speaks during the London 11 countries "Friends of Syria" meeting in Doha June 22, 2013. Western and Arab opponents of Bashar al-Assad met in Qatar on Saturday to tighten coordination of their stepped up support for rebels battling to overthrow the Syrian president. REUTERS/Mohammed Dabbous (QATAR - Tags: POLITICS CONFLICT)
Hoto: Reuters

A cikin ministocin har' da John Kerry na Amirka da kuma Laurent Fabius na Faransa, waɗanda suka gargaɗi Iran da ƙungiyar Hizbollah da ta daina ba da agaji na makamai ga gwamnatin Bashar Al-Assad.

Gabanin taron ministan harkokin wajen Birtaniya Williiam Hague da ya ke yin magana da' yan jaridu, ya ce har yanzu ba su bai wa 'yan tawayen na Siriya makamai ba. Kafin wannan taro wani kakakin ƙungiyar 'yan tawaye ya sanar da cewar sun fara samun man'yan makamai daga ƙasashen duniya, waɗanda suka haɗa da masu kakkaɓo jiragen sama na yaƙi da kuma tankokin yaƙi.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman