1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawar kafa gwamnatin hadin kai Falasdinawa ta kafe

November 30, 2006
https://p.dw.com/p/BuZb

Tattaunawar da ake yi tsakanin kungiyoyin Fatah da Hamas da nufin kafa wata gwamnatin hadin kan kasa ta cije. An jiyo haka ne daga bakin shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas a ganawar da yayi da sakatariyar harkokin wajen Amirka C-Rice a birnin Jericho na Gabar Yamma da Kogin Jordan. Rice ta godewa Abbas game da rawar da ya taka wajen kulla shirin tsagaita wuta na baya bayan a Zirin Gaza. Yanzu haka dai Amirka na fatan ganin an fadada shirin tsagaita wutar a dukkan yankunan Falasdinawa. Dr. Rice ta kuma tabo batun kafa wata kasar Falasdinawa mai ´yancinta.