1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawar samo bakin zaren warware rikicin yankin Darfur a Nigeria

Ibrahim SAniOctober 4, 2005

Ana ci gaba da tattauna samo hanyar warware rikicin daya fi kowa ne rikici dadewa a can birnin Abujan tarayyar Nigeria

https://p.dw.com/p/BvZD

Ya zuwa yanzu dai masu shiga tsakani daga bangaren kungiyyar hadin kann nahiyar Africa wato Au sun amince aci gaba da wannan tattaunawa a birnin na Abuja dake tarayyar ta Nigeria duk kuwa da rikice rikice da tashe tashen hankula dake faruwa a wannan yanki na Darfur.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa rasuwar mutane 32 a yan makonnin nan da muke ciki a yankin na Darfur da kuma kurarin da wani bangare na kungiyyar yan tawaye ta SLM tayi na ficewa daga zauren wannan taro a yanzu haka na neman tsunduma wannan taro a wani hali na kaka ni kayi.

A dai tun farkon fara wannan taro mai shiga tsakani daga kungiyyar ta Au wato Salim Ahmed Salim ya shaidawa yan jaridu cewa taron zai ci gaba a daya bangaren kuma aci gaba da kokarin shawo kann yan kungiyyar ta SLM don kada su fice daga wannan taro na zagaye na shida da a lokacin ne ake sa ran kwalliya ka iya biyan kudin sabulu.

Kungiyyar ta Au dai tace kusan a yanzu dukkannin bangarorin biyu na take yarjejeniyar tsagaitawa da bude wuta da aka cimma,musanmamma a inda kungiyyar ta Au tace bangaren gwamnati na daurewa larabawan nan masu tawaye gindi wajen kaiwa fararen hula hare hare a yankin na Darfur.

Salim Ahmed Salim wanda ya daukaka kira ga bangaren gwamnati da kuma na yan tawayen dasu martaba yarjejeniyar da aka cuimma ta tsagaitawa da bude wuta, ya kara da cewa taron zai ci gaba da tattauna yadda za a raba madafun iko da kuma albarkatun kasa da Allah ya huwacewa kasar a lokacin wannan taro. Har ilya yau Salim Ahmed Salim ya kara da cewa wannan zaure zai kuma tattauna batun harkokin tsaro da kuma yadda za a inganta shi a ranar 15 ga watan nan da muke ciki.

Shi kuwa jakada na musanman na Amuirka a kasar ta Sudan wato Roger Winter bayyana bacin ransa yayi game da wannan kurari da kungiyyar yan tawaye ta SLM tayi na kokarin ficewa daga wannan taro,to amma duk da haka yaci alwashin cewa da alama a wannan karo kwalliya ka iya biyan kudin sabulu.

A daya hannun kuma ministan harkokin wajen kasar Chad, cewa tuni gwamnatin kasar sa ta bayar da umarnin rufe ofishin jakadancin ta dake yammacin yankin na Darfur tayi a sabili da rikici daya ki ci yaki cinyewa.

Shi kuwa a nasa bangaren, faraministan kasar Holland Jan Peter Balkenende janyo hankalin bangarorin biyu yayi da cewa lokacin na neman kure musu, a don haka akwai bukatar yin karatun mun natsu don daukar matakan gaggawa na cimma sulhu don kawo karshen wannan rikici da yayi sanadiyyar rayukan alumma masu yawan gaske.

Shugaban dai na Holland ya fadi hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabi ga wakilan wannan taro a can Birnin na Abuja a yau talatar nan.

Bugu da kari Jan Peter Balkenende yaci gaba da cewa akwai babban nauyi na mutanen Sudan da kuma ma duniya baki daya akan wakilan dake halartar taron na ganin an samo bakin zaren warrware wannan rikici domin kowa ya huta da irin barnar dake faruwa a wannan yanki.

Kasar dai ta Holland na daga cikin kasashe na kungiyyar hadin kann turai wato Eu da kasashen arewacin Amurka dake bada gudummawa ta bangarori daban daban don samo bakin zaren wannan balahira dake faruwa a yankin na Darfur.

Ya zuwa yanzu dai daga dukkannin alamu a cewar rahotannin da suka iso mana dukkannin wadan nan bangarori guda biyu sun nuna fatan su na kawo karshen wannan rikici na yankin na Darfur a lokacin wannan tattaunawa dake a matsayin zagaye na shidda a tun lokacin da aka fara ta.

Wannan rikici dai na yankin na Darfur da aka shafe kusan watanni talatin ana yi a yanzu haka yayi sanadiyyar rayuka bayin Allah kusan dubu dari uku, da yawa yawan su kuma fararen hula