1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tawagar Jamus ta isa kasar Amirka

October 30, 2013

Wakilan Jamus za su gana da jami'an kasar Amirka kan zargin leken asirin da aka yi wa shugabar gwamnati.

https://p.dw.com/p/1A95a
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Wata tawagar manyan jami'an kasar Jamus ta isa birnin Washington na kasar Amirka, domin neman karin bayani kan zargin satar sauraron wayar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, wanda ake yi wa jami'an leken asirin Amirka.

Steffen Seibert kakakin Merkel, ya ce wakilan tawagar za su gana da hukumomin leken asiri na Amirka da kuma fadar gwamnatin kasar. Sannan akwai wata tawagar ta biyu da za ta isa kasar ta Amirka, duk kan wannan batu.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu