1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar The Greens ta sha gaban ta Merkel a Jamus

April 25, 2021

A Jamus jam'iyyar Greens ta masu rajin kare muhalli ta yi wa jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel fintinkau a sabon binciken jin ra'ayin jama'a da aka fitar da sakamakonsa a wannan Lahadi.

https://p.dw.com/p/3sXof
Grüne Kanzlerkanddidatin Annalena Baerbock
Hoto: Christian Thiel/imago Images

Jaridar Jamus ta Bild am Sonntag ta ruwaito cibiyar Kantar opinion research institute wace ta shirya binciken na cewa jam'iyyar Greens ta samu kaso 28 cikin 100 na mutanen da ta tuntuba a kan jam'iyyar da suke ganin za ta iya lashe Zaben Jamus da za a yi a watan Satumba mai kamawa.

Cibiyar ta ce jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ce ta zo ta biyu da kaso 27 yayin da jam'iyyar SPD ta ministan kudin Jamus ta samu kaso 13. Cibiyar dai ta gudanar da wannan binciken jin ra'ayin jama'a ne a tsakanin mutane 1,225 da ke nan Jamus a tsakanin 15 zuwa 23 ga wannan wata.

A ranar Litinin din da ta gabata ne jam'iyyar Greens din ta nada jagorarta Annalena Baerbock a matsayin 'yar takarar shugabar gwamnati, yayin da kawancen jam'iyyun CDU da CSU masu mulki suka tsayar da Armin Laschet sai kuma SPD da ta tsayar da Ministan Kudin Jamus Olaf Scholz a matsayin dan takararta.