1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Theresa May ta gaza gamsar da shugabannin EU

Mohammad Nasiru Awal
December 14, 2018

Firaministar Birtaniya Theresa May, ta gaza shawo kan shugabannin kungiyar Tarayyar Turai wajen daidaita batun ficewar kasarta daga kungiyar.

https://p.dw.com/p/3A9A5
Theresa May tare da shugaban hukumar Turai, Jean-Claude Juncker
Theresa May tare da shugaban hukumar Turai, Jean-Claude JunckerHoto: Reuters/Y. Herman

Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai sun kammala taron kolinsu na karshen shekara inda suka jaddada ci gaban da aka samu a kan manufarsu dangane da 'yan gudun hijira, suna bayyana cewa za su ci gaba a kan wannan turba.

Sai dai batun yarjejeniyar fitar kasar Birtaniya daga kungiyar shi ya mamaye tattaunawar da shugabannin suka kwashe kwanaki biyu suna yi a birnin Brussels na kasar Belgium.

A cikin wata sanarwa da suka fitar lokacin da suke rufe taron kolin na yini biyu da ke zama na karshe a wannan shekara, shugabannin na kasashen kungiyar Tarayyar Turan sun ce manufofinsu dangane da 'yan gudun hijira sun taimaka matuka wajen rage yawan sabbin zuwa a kasashen kungiyar EU idan aka kwatanta da shekarun 2015 zuwa 2016 lokacin da kwararar 'yan gudun hijirar ta kai kololuwarta.

To sai dai batun ficewar kasar Birtaniya daga kungiyar EU da ake wa lakabi da Brexit, shi ya mamaye zaman tattaunawar, inda Firaministar Birtaniya Theresa May ta kasa shawo kan shugabannin EU da su sake yin wata tattaunawa kan yarjejeniyar Brexit. To amma May ta fada wa wani taron manema labarai a birnin Brussels cewa tana sa rai za a gudanar da wasu jerin tattaunawa da EU kan Brexit din a cikin kwanaki masu zuwa.

Theresa May bei dem EU Gipfel
Hoto: Getty Images/D. Kitwood

Hakan na faruwa ne lokacin da Mrs. May ke cewa tana bukatar karin tabbaci kafin samun amincewar majalisar dokokin Birtaniya dangane da batun. A cewar Theresa May, cikin kwanaki nan gaba za ta sake zama da shugabannin na Turai domin daddale batun.

 

Ta kuma musanta wasu rahotannin da ke cewa jagororin na Turai sun bijire wa bukatun da ta gabatar na neman tabbacinsu kafin samun amincewar majalisar Birtaniya. Adawa da yarjejeniyar Brexit a Birtaniya ta mayar da hankali kan wani tsari na kariya da zai bar kan iyakarta a lardin Ireland ta Arewa da jamhuriyar Ireland a bude har sai an cimma sabuwar yarjejeniyar kasuwanci tsakanin Birtaniya da EU.

Wani daftari na farko dai ya ce a shirye EU take ta duba ko akwai yiwuwar ba da karin tabbaci dangane da batun na kariya ta kan iyakar, amma daga bisani an cire wannan bangare daga sanarwar bayan taron, lamarin da wata majiyar EU ta ce jami'ai sun fusata ganin yadda Firaminista May ta bar zauren taro hannu banza, amma duk da hakan May ta yi maraba da sanarwar hadin gwiwar.