1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon shafin sada zumunta na Trump

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 22, 2022

Tsohon shugaban kasar Amirka Donald Trump ya kaddamar da sabon shafinsa na sada zumunta, wanda ya yi wa lakabi da "Truth Social" tare da samar da shi a kan manhajar nan ta Apple's App store.

https://p.dw.com/p/47OZh
Trump ya kaddamar da shafinsa na „Truth Social“
Tsohon shugaban kasar Amirka Donald Trump Hoto: Mehmet Kaman/AA/picture alliance

Wani daga cikin ma'aikatan shafin na "Truth Social," ya nunar da cewa ana sa ran shafin zai fara aiki ka'in da na'in a karshen watan Maris mai zuwa. Shafukan sada zumunta na zamani da suka hadar da YouTube da Twitter da kuma Facebook, sun dakatar da Trump har na tsawon sama da shekara guda biyo bayan harin da magoya bayansa suka kai a ginin majalisar dokokin Amirka na Capitol a ranar shida ga watan Janairun bara. Trump wanda ya bayyana cewa sabon shafin nasa zai bayar da damar 'yancin fadar albarkacin baki, an zarge shi da tunzura magoya bayan nasa da suka kai harin na Capitol.