1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump na takun saka a kan Birnin Kudus

Suleiman Babayo
December 21, 2017

Amirka ta yi barazanar katse taimakon kudade ga kasashen da suka kada kuri'ar rashin amince da matakin kasar kan Birnin Kudus a matsayin fadar gwamnatin Isra'ila.

https://p.dw.com/p/2pkFo
USA - Präsident Trump - Jahresrückblick
Hoto: Reuters/J. Ernst

Shugaba Donald Trump na Amirka ya yi barazanar katse kudaden taimakon raya kasa ga duk wata kasa mamba a Majalisar Dinkin Duniya da za ta kada kuri'ar rashin amincewa da matakin gwamnatin Amirka game da ayyana Birnin Kudus a matsayin fadar gwamnatin Isra'ila.

A wannan Alhamis babban zauren Majalisar Dinkin Duniya zai yi zama na gaggawa, bayan tun fari a ranar Litinin Amirka ta kada kuri'ar naki a Kwamitin Sulhu na mjalisar ta dinkin duniya. Sai dai a babban zauren na mjalisar babu kuri'ar naki da ake bukata.

Kasashen Turkiya da Yemen suka bukaci zaman babban zauren na Majalisar Dinkin Duniya bisa bukata daga kungiyar kasashen Musulmai ta OIC. Jakadar Amirka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley ta yi barazanar rubuta sunan kasashen da suka nuna tirjiya ga matakin Amirka na amince da birnin Kudus a matsayin fadar gwamnatin Isra'ila, gabanin kammala shirin zaman lafiya na yankin Gabas ta Tsakiya.