1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya ce za a yi magudi a zaben Amirka

October 15, 2016

Dan takarar jam'iyyar Republican a zaben shugaban Amirka Donald Trump ya ce kafafen watsa labarai a Amirka na kokarin bada gudumawarsu wajen murde zabe shugaban kasa don Hillary Clinton ta samu nasara.

https://p.dw.com/p/2RGry
USA Rede Donald Trump in Miami
Hoto: Getty Images/J. Raedle

Trump na wadannan kalamai ne lokacin da ya ke jawabi ga magoya bayansa a New Hampshire a wani bangare na cigaba da yakin neman zabe. Dan takarar na jam'#yyar ta Republican ya ce tun ma ba a kai ga yin zaben ba kafafen watsa labarai na kasar sun rigaya sun murde shi inda suke yada karairayi game da shi da zantukan da ba su da tushe a wani yunkuri na ganin sun dora Hillary kan gadon mulki. A dan tsakanin nan Mr. Trump na shan suka daga abokan hamayya da 'yan kasar kan batun cin zarafin wasu mata ake zargin ya yi a shekarun da suka gabata, zargin da Trump din ya musanta.