1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya fadada matakin korar baki daga Amirka

Salissou Boukari
February 22, 2017

Ma'aikatar tsaron cikin gida ta kasar Amirka, ta bada wani sabon umarni ga jami'an kula da shigi da fici na 'yan sanda da kuma kwasta da su kama duk wanda bashi da takardun zama a kasar.

https://p.dw.com/p/2Y1Iq
USA Festnahmen bei US-Razzien gegen Einwanderer
'Yan sanda sun soma kama marasa takardun zama a AmirkaHoto: picture alliance/U.S. Immigration and Customs Enforcement/AP/dpa/C. Reed

Wannan mataki dai ya kasance ne daidai da kudirin da Shugaba Donald Trump ya dauka ranar 25 ga watan Janairu kan wadanda ba su da takardun zaman kasa a Amirka. Sai dai sabon umarnin bai shafi wadanda ba su da takardun zaman kasar da aka shigo da su suna 'yan yara kanana ba.

Wannan sabon mataki ya kara karfafa fargaba a tsakanin 'yan gudun hijirar da ba su da takardun zaman kasar ta Amirka. Da yake magana kan wannan sabon mataki, magajin garin birnin New York Bill de Blasio, ya ce wannan mummunan sauyin da aka samu na kai tsaye, na a matsayin cikakkar shaidar cewa burin da gwamnatin Shugaba Trump ta sa wa gaba shi ne na raba iyalai tare da saka tsoro da fargaba a tsakaninsu.