1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya sa baki a rikicin yankin Gulf

Ramatu Garba Baba
July 14, 2017

Shugaba Donald Trump ya tattauna da sarki Salman na kasar Saudiyya kan hanyar da za a bi na warware takaddamar diflomasiyyar da ke a tsakanin kasar Katar da wasu manyan kasashen yankin Gulf.

https://p.dw.com/p/2gaNA
Saudi Arabien Trump und König Salman bin Abdulaziz  Al Saud
Hoto: picture alliance/AA/B. Algaloud

Fadar White House ta sanar da tattaunawar da shugaba Donald Trump ya yi da sarki Salman na Saudiyya, inda sanarwar ta yi karin bayani kan batun warware rikicin kasar Katar da wasu kasashen yankin Gulf hudu, kan zargin da ake yi wa Katar na tallafawa harkokin ta'addanci. An dai yi tattaunawar ce ta wayar tarho wanda ke zuwa bayan ziyarar da sakataren harkokin wajen Amurkan Rex Tillerson ya kai yankunan na Larabawa.

Kasashen Larabawa sun zabi yanke hulda da kasar Katar bisa zarginta da tallafawa kungiyoyi na masu tada kayar baya, zargin da Katar ta musanta.