Trump ya sa dokar ta baci kan Mexiko
February 15, 2019Talla
Trump ya ce matsalar tsaro da ke faruwa a kan iyakar Mexico da Amirkan ta tsananta kuma za ta iya shafar tsaron kasa, a dangane da haka wajibi a samar da kudin gina katangar a tsakanin kan iyakokin kasashen biyu, ko da kuwa kudurin zai fuskanci tirjiya a majalisa da kuma kotu ya na mai cewa: "Na sa hannu kan dokar, kuma na sani mataki na gaba shi ne a kai batun kotu, kuma za mu iya gaza yin nasara a matakin farko. Amma daga karshe za mu karkare a kotun koli, inda muke fatan samun nasarar."