1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya zama zababben shugaban Amurka

November 9, 2016

Tuni dai abokiyar takararsa ta jam'iyyar Demokrat Hillary Clinton ta mika masa sakon taya murna. A ya yin da shugabannin kasashen duniya ke ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan sakamakon zaben.

https://p.dw.com/p/2SODm
USA Präsidentschaftswahl Donald Trump
Hoto: Getty Images/AFP/M. Ngan

Hamshakin mai kudin nan Donald Trump ya tasamma zama shugaban Amirka yayin da sakamakon da ya ke samu daga kirgen kuriun da ake kawo yanzu ya sha gaban Hillary Clinton a zaben ranar Talata mai cike da tarihi, abin da ke zama barazana ga kasuwar hada-hada ta duniya da ma ke girgiza magoya bayan Clinton a ciki da wajen Amirka.

Bayan rufe mazabun kada kuri'a, kafafan yada labarai na bin sakamakon daga jiha zuwa jiha inda Trump ya yi gaba da jihohin Ohio, da Florida da North Carolina.

Abin da ake bukata na yawan wakilan mazabu shi ne 270ga kowane dan takara ya zama shugaban Amirka  wanda kawo yanzu Trump ya samu sama da 260 yayin da Clinton ke da sama da 2015.

Nasarar da Trump ke samu dai na sake nuna yadda Amirkawa kansu ke rabe kan harkokin zamantakewa da al'ada da ma batun 'yan gudun hijira.