1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump zai gana da shugaban Falasdinawa

Yusuf Bala Nayaya
April 19, 2017

Da ya ke ganawa da manema mai magana da yawun fadar ta White House Sean Spicer ya ce wannan dama ce ga Shugaba Donald Trump da Mahmoud Abbas su nemi mafita kan rikincin Isra'ila da Falasdinawa.

https://p.dw.com/p/2bY0Y
USA Trump zu Angriff in Syrien
Hoto: picture-alliance/dpa/AP/A. Brandon

Shugaba Donald Trump na Amirka zai karbi bakunci na Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ranar uku ga watan Mayu kamar yadda  fadar White House ta bayyana a ranar Laraban nan.

Da ya ke ganawa da manema magana da yawun fadar ta White House Sean Spicer ya ce wannan dama ce da Shugaba Donald Trump da Mahmoud Abbas za su yi amfani da ita wajen lalubar hanyoyi da za su kai ga warware matsalar da ta ki ci taki cinyewa tsakanin Falasdinawa da 'yan Isra'ila.